Sai a Kiyaye: Gwamnan Kano Ya Fadi Hukuncin da Zai Fara Yiwa Masu Kin Biyan Haraji
- Gwamnatin Kano za ta fara gurfanar da masu kauce wa biyan haraji a 2025 da nufin gyara harkar tara kudaden shiga na jihar
- Hukumar tattara haraji ta Kano (KIRS) na fatan tara fiye da Naira biliyan ashirin a kowanne zango a shekarar 2025 mai kamawa
- Gwamna Abba Yusuf ya kawo sabon tsarin karɓar haraji da zai taimaka wajen aiwatar da manyan manufofin gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta fara hukunta masu kauce wa biyan haraji a shekarar 2025.
Wannan sanarwar ta fito daga mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, yayin wani taro da aka gudanar a Kaduna.
Kano: KIRS ta gargadi masu kin biyan haraji
Dakta Zaid Abubakar, shugaban hukumar kula da haraji ta jihar Kano (KIRS), ya bayyana hakan yayin da yake yiwa gwamnan bayani a wani taron masu ruwa da tsaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwar da Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya rahoto Dakta zaid na cewa gwamnati za ta fara gurfanar da masu kin biyan haraji a kotu.
Shugaban hukumar KIRS ya ce an dauki matakin domin inganta dabarun tara haraji da tabbatar da bin dokokin haraji ba wai don karbar harajin kawai ba.
Abba ya na son tara N80bn a 2025
Hukumar ta KIRS ta na hasashen samun fiye da Naira biliyan ashirin a kowanne zango na shekarar 2025.
A baya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallami shugaban hukumar KIRS da ya gada, sannan ya kafa sabon tsarin gudanarwa.
Sabon tsarin ya haɓaka aikace-aikacen hukumar haraji a watannin uku na karshe na shekarar 2024.
Gwamnan zai ƙaddamar da sabon tsarin karɓar haraji don samun ƙarin kuɗaɗe, wanda zai taimaka wajen cika alkawurran kamfen dinsa.
Farfesan Kano ya magantu kan gyaran haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani farfesa a jami'ar BUK Kano, Kabiru Dandago ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya yiwa kudurorin gyara harajinsa garambawul.
A yayin da ya nemi Tinubu ya kyale talakawan Najeriya su sarara kan kara kudin haraji, Farfesa Kabiru ya ce masu kudi ne ya kamata a karawa haraji.
Asali: Legit.ng