Bayan Faruwar Iftila'i a Najeriya, Tinubu Ya Soke Bukukuwan da Ya Shirya, Ya Jajanta

Bayan Faruwar Iftila'i a Najeriya, Tinubu Ya Soke Bukukuwan da Ya Shirya, Ya Jajanta

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nuna takaici bayan aukuwar iftila'in da ya yi sanadin mutuwar mutane a Abuja da Anambra
  • Shugaban ya soke bukukuwan da ya shirya a yau a jihar Lagos domin girmama wadanda lamarin ya rutsa da su
  • Hakan ya biyo bayan rasa rayuka a Abuja da Anambra yayin rabon kayan tallafi da na abinci saboda halin kunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Shugaba Bola Tinubu ya soke dukkan bukukuwan da aka tsara a jihar Lagos yayin da ya je hutu.

Tinubu ya dauki matakin ne sakamakon hatsaniya yayin rabon abinci da ya faru a Abuja da jihar Anambra.

Tinubu ya shiga damuwa kan iftila'in rasa rayuka a Najeriya
Bola Tinubu ya fasa gudanar da bukukuwan da ya shirya bayan rasa rayuka a Abuja da Anambra. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tallafi: An rasa rayuka Abuja da Anambra

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya tabbatar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Bayan tsokacin shugaban BUA, Dangote ya fadi matsayarsa kan matakan Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan mutuwar mutane da dama yayin hatsaniyar da ta afku a safiyar ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024.

An tabbatar da cewa mutane 10 sun mutu sanadin cunkoson rabon tallafi da wani coci a Abuja ya yi.

Daga bisani, rundunar yan sanda ta halarci wurin tare da kaddamar da bincike domin hana afkuwar hakan a gaba.

Tinubu ya jajantawa yan Najeriya kan lamarin

A cikin sanarwar, shugaban ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin takaici da cewa za a iya kaucewa hakan.

Daga bisani ya soke duk wani taronsa na yau a matsayin girmamawa ga wadanda suka rasa rayukansu.

“Shugaba Bola Tinubu ya soke dukkan bukukuwan da ya shirya na yau a jihar Lagos, ciki har da halartar bikin Lagos Boat Regatta na 2024 domin girmama wadanda hatsaniyar ta rutsa da su a Abuja da jihar Anambra."

- Cewar sanarwar

Kara karanta wannan

Ana fargabar rasa rayuwa a turereniyar karbar kayan tallafi a Abuja, wasu suna asibiti

Rabon tallafi: Mutane 27 sun mutu a Anambra

Kun ji cewa ana fargabar akalla mutum 27 sun mutu a Okija yayin rabon shinkafar Kirsimeti da wata gidauniya ta shiryawa talakawa.

Bidiyo ya nuna yadda kyakkyawan niyyar rabon tallafin ta rikide zuwa masifa, inda mutane suka mutu, wasu suka jikkata.

Hadimin gwamnan Anambra ya rasa ‘yan uwa biyu a cikin lamarin, yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da faruwar turereniyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.