'Abin da Zai Jawo Tunkuda Keyar Sarakunan Gargajiya Gidan Kaso Nan Take'

'Abin da Zai Jawo Tunkuda Keyar Sarakunan Gargajiya Gidan Kaso Nan Take'

  • Gwamnatin jihar Ondo ta sha alwashin daukar mummunan mataki kan wasu sarakunan gargajiya kan laifin kwace filaye
  • Gwamnatin ta nuna damuwa kan yadda ake samun sarakunan da jawo rigima kan batun filaye a yankunansu
  • Kwamishinan shari'a, Dr. Kayode Ajulo shi ya tabbatar da haka inda ya kuma gargadi sarakunan kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ta yi bazaranar tura wasu sarakunan gargajiya gidan kaso.

Kwamishinan Shari’a a jihar, Dr. Kayode Ajulo ya ce duk wani basarake da aka samu da laifin kwace filaye za a tura shi gidan yari.

Gwamna ya yi barazanar tura sarakunan gargajiya gidan kaso
Gwamnatin jihar Ondo ta fadi laifin da zai tura sarakunan gargajiya gidan kaso. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Gwamna ya gargadi sarakunan gargajiya a Ondo

Ajulo ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani kan dokar hana kwace filaye da ke gaban Majalisar Dokokin jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fita daban a Najeriya, ya ba ma'aikatan gwamnati hutun kwanaki 7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya ce wasu daga cikin sarakunan gargajiya na da hannu wajen kwace filaye.

“Gwamnati ba za ta ji tsoron nunawa kowa yatsa ba, zan fada a fili, wasu daga cikin sarakunanmu sun jawo matsaloli masu yawa a batun kwace filaye."
“Ko suna zaune a fadarsu, suna aika mutane don tayar da tarzoma, muna ganin yadda suke amfani da makamai suna raunata juna."
“Idan aka kama wasu daga cikin sarakunan da laifi, tare da kai su gidan yari saboda wannan batu, babu wanda ya kamata ya koka."

- Kayode Ajulo

Matakan da gwamna ya dauka a Ondo

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya rattaba hannu kan dokar gudanarwa don magance matsalar kwace filaye.

A cewarsa, akwai bukatar magance wannan barazana yadda ya kamata duba da matsalolin da ke cikinta.

Tsohon gwamnan Ondo ya rasu

Kun ji cewa Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya yi alhinin rasuwar tsohon gwamnan soji na farko na Jihar Ondo, Kyaftin Ita David Ikpeme.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Marigayi Ikpeme ya rasu yana da shekara 89 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a makon nan.

Gwamna Aiyedatiwa ya yabawa gudunmawar da Ikpeme ya bayar wajen gina tubalin ci gaban jihar Ondo tun daga 1976 zuwa 1978.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.