An Shiga Tashin Hankali, Mutane 27 Sun Mutu a Turereniyar Karbar Shinkafar Sadaka

An Shiga Tashin Hankali, Mutane 27 Sun Mutu a Turereniyar Karbar Shinkafar Sadaka

  • Ana fargabar akalla mutum 27 sun mutu a Okija yayin rabon shinkafar Kirsimeti da wata gidauniya ta shiryawa talakawa
  • Bidiyo ya nuna yadda kyakkyawan niyyar rabon tallafin ta rikide zuwa masifa, inda mutane suka mutu, wasu suka jikkata
  • Hadimin gwamnan Anambra ya rasa ‘yan uwa biyu a cikin lamarin, yayin da ‘yan sanda suka tabbatar da faruwar turereniyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Akalla mutum 27 ne suka rasa rayukansu a wajen turereniyar da ta faru a Okija, karamar hukumar Ihiala, jihar Anambra.

Wannan mummunan lamari ya faru ne yayin rabon shinkafar Kirsimeti da wata gidauniya ta shirya don tallafa wa marasa galihu.

Ganau sun bayyana yadda mutane suka mutu a wajen rabon tallafin shinkafa a Anambra
Mutane 27 ne ake fargabar sun mutu a wajen karbar tallafin shinkafa a Anambra.
Asali: Original

Mutane sun mutu a wajen rabon shinkafa

Wata gidauniya da fitaccen ɗan siyasa kuma jigon APGA, Cif Ernest Obiejesi, wato Obijackson, ya kafa ce ta shirya rabon tallafin a cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rasa rayuwa a turereniyar karbar kayan tallafi a Abuja, wasu suna asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau ya bayyana yadda kyakkyawar niyyar rabon shinkafar ta juye zuwa mummunar masifa sakamakon dandazon mutanen da suka halarta.

Wani faifan bidiyo da ya yadu ya nuna mummunar turereniyar, wadda ta jawo mutane 27 suka mutu tare da jikkata wasu da dama.

Hadimin gwamna ya rasa 'yan uwa 2

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙauyen, yayin da gawarwakin waɗanda suka mutu aka kai su dakin ajiyar gawa.

The Nation ta rahoto cewa lamarin ya shafi gwamnati, inda wani hadimin Gwamna Chukwuma Soludo ya rasa ‘yan uwa biyu a cikin turereniyar.

Ba a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Tochukwu Ikenga ba amma wani babban jami’in ‘yan sanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mutane sun mutu a turmutsutsun Abuja

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto cewa mutane da dama ake fargabar sun mutu yayin da wasu suka jikkata a birnin tarayya Abuja.

An ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke turereniyar karbar tallafin abinci na bikin Kirsimeti da Cocin Holy Trinity Catholic da ke Maitama ta shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.