Ziyarar Zulum a Diffa: 'Yan IDP 20 sun mutu yayin turereniyar karbar abinci da kudi

Ziyarar Zulum a Diffa: 'Yan IDP 20 sun mutu yayin turereniyar karbar abinci da kudi

Mutane ashirin, yawancinsu mata da kananan yara, sun mutu yayin turereniya a wurin rabon abinci da kudi a sansanin 'yan gudu hijira (IDP) da ke garin Diffa, kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Kazalika, karin wasu mutane 12 sun samu rauni yayin ziyarar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum, a zuwan da ya yi domin ganawa da mazauna sansanin 'yan asalin Najeriya.

"Muna da adadin mutane 20 da suka mutu," a cewar wani ma'aikacin lafiya, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Ma'aikatan lafiya sun tabbatar da cewa mutane 12 sun samu rauni.

Turereniyar ta faru ne a cibiyar al'adu da garjiya (MTC) a Diffa, daya daga cikin wuraren da aka tsara gwamna Zulum zai kai ziyara a ziyararsa ta ranar Litinin.

Gwamna Zulum ya ziyarci kasar Nijar ne domin raba kayan tallafi ga mazauna sansanin da aiyukan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram suka tagayyara.

Ziyarar Zulum a Diffa: 'Yan IDP 20 sun mutu yayin turereniyar karbar abinci da kudi
Zulum yayin ziyarar garin Auno bayan an kai hari
Asali: Facebook

Shaidar gani da ido ya ce ba a samu matsala ba a rana ta farko da aka yi rabon kayan, amma a rana ta biyu da labari ya zagaya cewa an yi rabo sai jama'a suka yi tururuwar zuwa sansanin, lamarin da ya haddasa turereniya a ranar.

DUBA WANNAN: Sai an yi zagaye na biyu: Kwamitin dattijai ya soke zaben da aka yi a kan kyakyawar budurwa, Khadija, a Bauchi

Gwamnan jihar Difa da shugaban majalisa sun ziyarci asibitin da aka ajiye gawar mutanen, sannan sun ziyarci wadanda suka samu rauni, amma babu wanda a cikinsu ya fitar da wani jawabi.

Amma masu nazarin al'amura nada ra'ayin cewa turereniyar da mazauna sansanin gudun hijirar suka yi, wata alama ce da ke nuna cewa suna fama da matsananciyar yunwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng