Ana Fargabar Rasa Rayuwa a Turereniyar Karbar Kayan Tallafi a Abuja, Wasu Suna Asibiti

Ana Fargabar Rasa Rayuwa a Turereniyar Karbar Kayan Tallafi a Abuja, Wasu Suna Asibiti

  • Ana fargabar rasa rayuka da kuma samun raunuka yayin raba kayan tallafi a wani coci da ke birnin Abuja
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar yara bakwai yayin turereniya domin samun kayan tallafin saboda halin kunci
  • Hakan bai rasa nasaba da halin matsin tattalin arziki da aka shiga da ake zargin hakan ya faru saboda matakan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Akalla mutane 10, ciki har da yara ake fargabar sun mutu yayin turereniyar karbar kayan tallafi.

Rahotanni sun tabbatar cewa da dama sun samu raunuka a yayin cunkoson a Cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, Abuja.

An rasa rayuka yayin raba kayan tallafi a Abuja
Mutane 10 ciki har da yara sun mutu yayin rabin kayan tallafi a Abuja. Hoto: Legit.
Asali: Original

Rabon tallafi: Ana fargabar rasa rayuka Abuja

Vanguard ta ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 21 ga watan Disambar 2024 a birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

'Abu ya zo da ƙarar kwana': Wani jami'an tsaro ya riga mu gidan gaskiya a bakin aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya faru ne yayin da dubban mazauna yankin ke kokarin samun kayan tallafi da cocin ke rabawa.

An shirya taron domin tallafawa mazauna yankin da ke fama da kunci inda sama da mutane 3,000 da ke kusa suka zo.

Cocin ya yi magana kan faruwar lamarin

Daraktan sadarwa a Cocin, Padre Mike Nsikak Umoh ya tabbatar da faruwar wannan mummunan al’amari.

“Eh tabbas gaskiya ne game da lamarin, amma cikakken bayani bai fito ba."

- Padre Mike Nsikak Umoh

Wani ganau ya bayyana yanayin a matsayin mummunan tashin hankali, inda ya ce akalla yara bakwai sun mutu.

Yawancin mutanen sun iso wurin tun karfe 4:00 na safe domin samun rabonsu na kayan tallafin, cewar Daily Post.

Turereniyar ta faru ne tsakanin karfe 7:00 zuwa 8:00 na safe yayin da hakan ya jawo matsala da samun raunuka.

Dalibai sun mutu yayin rabon shinkafa

Kun ji cewa Ɗalibai da dama sun mutu a wurin da gwamnatin jihar Nasarawa ta shirya rabon tallafin abinci ga ɗaliban jami'ar jihar.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya ce bayan Wike ya kwace filinsa da na wasu manya a Abuja

Rahoto ya nuna cewa tun da asubahi ɗaliban suka mamaye wurin da aka shirya rabon, suka kutsa cikin rumbun ajiyar da karfi.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban jihar Nasarawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.