'Yar Gwagwarmaya Ta Hango Lokacin da Tinubu Zai Mutu, Kotu Ta Tura Ta Gidan Yari

'Yar Gwagwarmaya Ta Hango Lokacin da Tinubu Zai Mutu, Kotu Ta Tura Ta Gidan Yari

  • Babbar kotun Abuja ta garkame 'yar gwagwarmaya, Olamide Thomas kan maganganun da ta yi a sohiyal midiya kan Seyi Tinubu
  • Thomas na fuskantar tuhume-tuhume uku da suka haɗa da cin mutunci, barazana, da tayar da hankalin dan shugaban kasa
  • Kotun ta dage sauraron karar Olamide Thomas zuwa ranar 30 ga Disamba don ci gaba da shari’ar da ta shafi sufetan 'yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsare Olamide Thomas, mai rajin kare hakkin dan Adam da ake tuhuma da zagi da bata suna.

Masu shigar da kara na zargin Olamide Thomas da zagin dan shugaban kasa da sufetan 'yan sanda ayode Egbetokun a shafukan sada zumunta.

Kotu ta yi hukunci kan yar gwagwarmayar da ta zagi Tinubu a soshiyal midiya
Kotu ta garkame 'yar gwagwarmaya kan zagin Tinubu da sufetan 'yan sanda. Hoto: @firstladyship, @PoliceNG
Asali: Twitter

Kotu ta garkame mai zagin Tinubu

A ranar Juma’a, alkalin kotun, Emeka Nwite, ya ki karɓar roƙon beli da lauyan Thomas ya gabatar ta baki a kotu, a cewar rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya umurci lauyan da ya gabatar da takardar neman beli ta hanyar da ta dace.

An gurfanar da Thomas kan tuhume-tuhume uku da suka shafi cin zarafi ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

Thomas ta musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake mata a gaban kotu.

Tuhume tuhume 3 da ake yi mata

'Yan sanda sun zargi Thomas da wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda ta ce, "Seyi Tinubu zai mutu a wannan shekara."

Tuhumar ta biyu ta ce ta yi barazana da cin mutuncin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a cikin bidiyon.

A tuhumar ta uku, an zarge ta da fadin cewa, "’Ya’yan Muyiwa Adejobi za su mutu a gabansa."

Kotun ta dage shari’ar zuwa 30 ga Disamba.

'Za a zage ku' - Tinubu ga ministoci

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya gargadi sababbin ministoci da su kasance cikin shiri, domin ƴan Najeriya na iya tsangwamar su.

Tinubu ya roƙe su su maida hankali kan ayyukansu don ceto ƙasa, bayan sun karɓi rantsuwar kama aiki a fadar shugaban ƙasa, Abuja, su toshe kunne daga jin zagin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.