Tinubu Ya Ware N27bn domin Rabawa Buhari, Jonathan da Mataimakansu a 2025
- Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a gaban Majalisar Tarayya a wannan mako
- Daga cikin kasafin kudin na 2025 akwai kudi kimanin N27bn da aka ware domin tsofaffin shugabannin kasa da mataimakansu
- Daga cikinsu akwai Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da kuma Cif Olusegun Obasanjo da mataimakansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ware zunzurutun kudi N27bn domin hakkokin tsofaffin shugabannin ƙasa.
Sauran wadanda za su ci gajiyar akwai tsofaffin mataimakan shugabannin ƙasa da shugabannin soji da shugabannin ma’aikata.
Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025
Binciken jaridar Punch ya tabbatar da cewa za a ba da kudin ne a sabuwar shekarar 2025 da za mu shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na daga cikin tsarin kasafin kuɗin shekarar 2025 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar a gaban Majalisa.
Kasafin kudin kimanin N49.70trn ya ba da fifiko kan tsaro da gine-gine da cigaban ɗan Adam da kuma sauran bangarori.
Sannan daga cikin kasafin akwai gibin kuɗi na Naira tiriliyan 13.39 da za a rufe ta hanyar aro wanda wasu yan Najeriya suka kushe kasafin da cewa bata lokaci ne.
Tsofaffin shugabannin kasa za su samu N27bn a 2025
Wadanda za su ci gajiyar akwai Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo.
Sannan akwai tsofaffin mataimakan shugabannin kasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo da Farfesa Yemi Osinbajo da sauransu.
Rahoton ya ce sauran sun haɗa da tsofaffin shugabannin sojoji, Janar Yakubu Gowon da Janar Abdulsalami Abubakar da Janar Ibrahim Babangida.
Buhari ya magantu da aka kwace filinsa
A baya, mun baku labarin cewa kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wanke shi kan kiran sunansa da ake yi kan filaye da aka kwace a Abuja.
Garba Shehu ya musanta cewa filin na Buhari ne kai tsaye inda ya ce Gidauniya ce ta magoya bayansa suka siya masa.
Kakakin tsohon shugaban ya ce watakila yayin cika takardu ne suka saba ka'idar hukumar FCTA da har ya kai aka kwace filin.
Asali: Legit.ng