Emefiele: Tsohon Gwamnan CBN Ya Sake Shiga Matsala, Kotu Ta Yi Hukunci
- Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa watau EFCC ta sake yin nasarar kwace wani babban wurin ajiya ƙai alaka da Godwin Emefiele
- Babbar kotun tarayya mai zama a Legas ta kwace gidan ajiyar tare da kadarorin da ke maƙare a ciki, ta miƙaws gwamnatin Najeria
- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN na ci gaba da fuskantar shari'a kan zargin da ya shafi zamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a Legas ta ƙwace wani babban gidan ajiyar kayayyaki da ke da alaƙa da tsohon gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele.
Ƙaton wurin ajiyar dai an gina shi ne a wani fili mai girman kadada 1.925 da ke kan babban titin Lagos zuwa Ibadan a Magboro.
Jaridar Daily Trust ta ruwaoto cewa katafaren gidan ajiyar kayan na ɗauke da wasu manya-manyan kwantenoni na karfe guda 54.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan CBN ya rasa dukiya
Lokacin da jami'an hukumar EFCC suka buɗe kwantenonin yayin bincike, sun gano cewa kekunan ɗinki ne makare a ciki.
Mai shari’a Deinde Dipeolu na kotun ya bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi bayan da EFCC ta gabatar da bukatar a kwace su ranar 28 ga Nuwamba.
Alkalin ya kuma amince EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta buga labarin kwace kadarorin na wucin gadi a jaridu domin wanda ke da ja da umarnin kotu ya kai ƙorafi.
Kotu ta yi hukunci kan batun wurin ajiyar
Hukumar EFCC ta bi umarnin kotun inda ta wallafa labarin a manyan jaridu ciki hada Daily Trust amma babu wanda ya zo ya ce kadarorinsa ne ko ya kawo ƙorafi.
Bayan haka ne hukumar ta sake komawa babbar kotun tarayya da buƙatar kwace kadarorin na har abada tare da mallakawa gwamnatin tarayya.
A ranar Alhamis alkalin kotun ya bayar da umarnin a kwace kadarorin da suka hada da kwantenonin da filayen tare da mallakawa gwamnatin Najeriya, rahoton Leadership.
Kotu ta ƙwace rukunin gidaje a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya ta ƙwace unguwa guda mao kunshe da gidaje sama da 750 a birnin tarayya Abuja.
Duk da ba a bayyana wanda ake zargin ya mallaki rukunin gidajen da aka ƙwace ba, an ce wannan ce nasara mafi girma da EFCC ta samu a lokaci ɗaya.
Asali: Legit.ng