Bayan Kwace Filayen Buhari da Wasu Yan Siyasa, Wike Ya Sake ba da Wa'adin Makwanni 2
- Bayan soke filayen manyan yan siyasa a Najeriya, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake ba da wa'adi kan matakin
- Nyesom Wike ya ba da tsawon makwanni biyu ga dukan wadanda ba su cika ka'ida ba su tabbatar sun bi doka
- Hakan na zuwa ne bayan kwace filayen yan siyasa da dama ciki har da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake ba da wa'adi ga wadanda aka kwace filayensu a birnin.
Wike ya ba mamallakan filaye 762 a unguwar Maitama II wa’adin makonni biyu su biya kuɗin takardun mallakar filayensu.
Nyesom Wike ya gargadi wadanda aka kwacewa filaye
Channels TV ta ce duk wadanda suka saba ka'ida kan wa'adin za su fuskanci matakin ƙarshe na soke mallakarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin Wike na musamman kan harkokin sadarwa, Lere Olayinka shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa.
Wike ya jaddada cewa, manufar gwamnatin ba wai a karɓe filayen mutane ba ne, amma a tabbatar da sun biya kuɗin da ya kamata ga gwamnati.
Wike ya ba su wa'adin makwanni 2
“A tuna cewa a ranar 5 ga Oktobar 2024, an fitar da sunayen mutane 3,273 da suka ci filaye amma ba su biya kuɗin takardun mallakarsu ba." "An ba su wa’adin makonni biyu su biya kuɗinsu ko kuma su rasa mallakar filayensu gaba daya."
"Daga cikin 3,273, mutane 2,511 sun cika wannan sharadi, inda aka bar 762."
- Cewar sanarwar
Har ila yau, sanarwar ta ce babu wani karin wa'adi daga ranar 3 ga watan Disambar 2025 saboda haka ake shawarartarsu su biya kudin kafin lokacin, cewar The Nation.
Buhari ya magantu bayan kwace filinsa
Kun ji cewa Kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wanke shi kan kiran sunansa da ake yi kan filaye da aka kwace a Abuja.
Garba Shehu ya musanta cewa filin na Muhammadu Buhari ne kai tsaye inda ya ce Gidauniya ce ta magoya bayansa suka siya masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng