Ta Tabbata: 'Yan Kasuwa Sun Sauke Farashin Man Fetur, Lita Ta Koma Kasa da N1060

Ta Tabbata: 'Yan Kasuwa Sun Sauke Farashin Man Fetur, Lita Ta Koma Kasa da N1060

  • Wasu gidajen mai a sassan Najeriya sun fara sayar da litar fetur a sabon farashi awanni bayan sanarwar matatar Dangote
  • An rahoto cewa Dangote ya rage farashin fetur daga N970 zuwa N899.50 kan kowace lita domin rage wahala ga 'yan Najeriya
  • Awanni bayan sanarwar matatar, MRS da wasu dillalai suma sun rage farashin litar fetur dinsu da kashi 11.8% daga N1,060

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Dillalan da suke sayo fetur daga matatar Dangote sun rage farashin da suke sayar da litar fetur a gidajen mansu da kusan kashi 11.8%.

An rahoto cewa gidajen mai mallakin wadannan 'yan kasuwar na sayar da litar fetur kan N939.50 maimakon farashin N1,060 na baya.

'Yan kasuwa sun sauke farashin man fetur bayan sanarwar rage farashin daga matatar Dangote
Giajen mai sun fara sayar da fetur a sabon farashi yayin da Dangote ya rage kudin man. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

'Yan kasuwa sun rage farashin fetur

Jaridar Vanguard ta tabbatar da cewa a jiya Alhamis, 19 ga Disamba 'yan kasuwar na sayar da litar fetur kan N1,060 amma a yau Juma'a wasu sun rage farashin zuwa N939.50.

Kara karanta wannan

Farashin shinkafa ya karye daga N84000, an fadi kasuwar da ake samunta da sauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin MRS da wasu manyan dillalai sun rage farashin su, amma shugaban MRS, Alhaji Sayyu Idris Dantata, ya ki yin tsokaci kan batun.

Ziyarar da aka kai gidan mai na MRS a Ojota, Legas, ta tabbatar da cewa sun fara sayarwa a N939.50 kowace lita.

Dangote ya fara sauke kudin man fetur

Matatar Dangote ta rage farashin mai daga N970 zuwa N899.50 a wani mataki na rage wahalhalu ga 'yan Najeriya.

Dangote ya bayyana cewa wannan ragin farashi zai saukaka tsadar sufuri musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.

Anthony Chiejina, jami'in Dangote Group, ya ce masu sayen mai za su iya samun damar sayan karin litoci idan suka kiyaye wasu sharuda.

NEMAN ta magantu kan farashin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar manyan dillalan man fetur ta MEMAN ta sanar da cewa an samu raguwar farashin shigo da man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Dangote: Farashin litar man fetur ya sauka a gidajen man ƴan kasuwa da NNPCL

MEMAN ta sanar da cewa farashin shigo da litar fetur ya ragu zuwa N970 a watan Disambar 2024 idan aka kwatanta da farashin N971 a Nuwambar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.