Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ya Shirya Kisan Sarkin Gobir Ya Mutu a Hannun Sojoji

Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ya Shirya Kisan Sarkin Gobir Ya Mutu a Hannun Sojoji

  • Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bako Wurgi, ya bakunci lahira kwanaki kadan bayan kama shi a sakamakon harbin bindiga
  • Ana zargin Bako Wurgi, na hannun damar dan ta'adda Bello Turji da kitsa kisan sarkin Gobir da sauran ayyukan ta'addanci
  • Kafin mutuwarsa, Wurgi ya ba sojoji muhimman bayanan sirri da za su taimaka wajen yaki da 'yan bindiga a Arewa ta Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bako Wurgi wanda sojojin Najeriya suka cafke a ranar 14 ga watan Disamba ya bakunci lahira.

An rahoto cewa, Bako Wurgi, na hannun damar dan ta'adda, Bello Turji ne ya kitsa sacewa da kuma kisan sarkin Gobir, Alhaji Isa Mohammad Bawa.

Manjo Janar Buba Edward ya yi magana kan mutuwar dan ta'adda, Bako Wurgi.
Dan bindiga Bako Wurgi ya bakunci lahira kwanaki kadan da cafke shi. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Hatsabibin dan bindiga Bako Wurgi ya mutu

Jaridar Punch ta rahoto runndunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa dan bindiga Bako Wurki ya sheka barzahu sakamakon harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da daraktan yada labaran hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Buba Edward ya fitar ranar Juma'a ta ce Wurgi ya mutu ne kwanaki bayan kama shi.

Sanarwar ta ce:

"Hakazalika, dakarun soji a Arewa ta Yamma sun cafke hatsabibin dan bindiga mai suna Bako Wurgi wanda ya gawurta a ayyukan ta'addanci."

Yadda Bako Wurgi ya mutu a hannun sojoji

Jaridar The Guardian ta rahoto Manjo Janar Buba ya ci gaba da cewa:

"Ana zargin hatsabibin shugaban 'yan bindigar da aka cafke (Bako Wurgi) shi ne ya kitsa kisan wani sarki a Sokto kuma babbar na hannun daman dan ta'adda Bello Turji ne.
"Rikakken dan ta'addan, Bako Wurgi, ya gamu da ajalinsa sakamakon raunukan da ya samu daga harbin bindiga.
"Sai dai kafin mutuwarsa, ya ba rundunar muhimman bayanan sirri wadanda za su taimaka wajen yaki da 'yan ta'addan."

Turji ya yi barazana kan kama Wurgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitinannen dan bindiga, Bello Turji ya fito yana kumfar baki bayan samun labarin cewa sojoji sun cafke Bako Wurgi.

Kara karanta wannan

Majalisa ta bukaci sakin shugaban Miyetti Allah, ta gayyaci hafsun tsaro

Bello Turji ya yi barazanar kai munanan hare hare a garuruwan Sokoto da Zamfara matsayin martani ga sojojin kasar nan kan cafke dan ta'adda, Wurgi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.