Dogo Gide, Najaja Sun Shiga Matsi da Bullar Lakurawa, Ana Hasashen Dagulewar Lamura

Dogo Gide, Najaja Sun Shiga Matsi da Bullar Lakurawa, Ana Hasashen Dagulewar Lamura

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa bayyanar Lakurawa a Arewa maso Yamma na barazana ga shugabannin yan bindiga
  • Wasu shugabannin yan bindiga sun shiga halin matsi yayin da Lakurawa ke ƙoƙarin mamaye ikonsu a yankin
  • Hakan ya biyo bayan bullar ƙungiyar a watannin baya da ya sake ta'azzara rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Zuwan Lakurawa a Arewacin Najeriya ya sake jefa yankin a wani sabon yanayi na rikice-rikicen ƴan bindiga.

Manyan shugabannin yan bindiga irin su Dogo Gide da Najaja na fuskantar barazana daga sabuwar ƙungiyar Lakurawa.

Yadda Lakurawa suka zama barazana ga shugabannin yan bindiga
Shugabannin yan bindiga na fuskantar barazana bayan bullar ƙungiyar Lakurawa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Lakurawa sun zama annoba ga yan bindiga

Rahotan Zagazola Makama ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta kafa sansani a Bagega da ke jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sha yabo kan kashe gagga gaggan 'yan bindiga, Manore da Lalbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin ƙungiyar na yunƙurin shigar da shugabannin yan bindiga cikin shirinsu domin kafa 'Kasar Musulunci'.

Sai dai kin amincewarsu da wannan yunƙuri ya haifar da tsamin dangantaka da kuma yiwuwar rikici mai tsanani da ake hasashen sabuwar arangama za ta kunno kai tsakaninsu.

Dogo Gide da Najaja sun tsinci kansu cikin matsi yayin da suke fuskantar barazanar Lakurawa, wanda hakan ka iya jefa su cikin rikici mai tsanani.

Zaman Lakurawa a yankin ba kawai barazana ce ga mulkin Gide da Najaja ba, har ma tana iya jawo karin matsin lamba daga dakarun tsaro.

Al’ummomin da ke yankunan suna cikin mawuyacin hali da addu’ar samun zaman lafiya daga hare-haren ƴan bindiga da kuma barazanar Lakurawa.

Masu kera bama-bamai sun kunno kai

Wani abin damuwa shi ne shigar wasu gungun mutane shida da suka ƙware wajen kera bama-bamai.

Wadannan mutane sun fito ne daga yankin Arewa maso Gabas zuwa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

Miyagun sun samu horo ne daga Nanaye, wani tsohon ƙwararren dan Boko Haram kan bama-bamai, wanda yanzu ya mika wuya.

An tabbatar da cewa wadannan mutane sun riga sun isa sansanin ‘yan ta’adda a jihohin Niger da Zamfara.

An rasa rayuka bayan arangama tsakanin yan bindiga

Kun ji cewa mummunan fada ya barke tsakanin tsagin yan bindiga a jihar Katsina wanda ya yi ajalin shugabanni uku.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gwabza fada ne a ranar Talata 17 ga watan Disambar 2024 a karamar hukumar Safana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.