NSCDC: Rundunar Tsaron Farar Hula Ta Tura Jami'ai 1850 zuwa Kogi, Ta Fadi Dalili

NSCDC: Rundunar Tsaron Farar Hula Ta Tura Jami'ai 1850 zuwa Kogi, Ta Fadi Dalili

  • Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta tura jami’ai 1,850 don tabbatar da tsaro a jihar Kogi yayin bukukuwan karshen shekara
  • Kwamandan NSCDC, ta gargadi matasa da su guji aikata laifuffukan da za su iya jawo masu fushin doka yayin bukukuwan
  • Esther Akinlade, ta kuma nemi al'ummar Kogi da su taimakawa jami'an tsaro da bayanai domin tabbatar da tsaro a fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Hukumar NSCDC ta tura jami’ai 1,850 domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan karshen shekara a jihar Kogi.

Abdullahi Aliyu, mai magana da yawun hukumar a Kogi, ya ce an zabo jami’an daga sassa daban-daban ciki har da Agro Rangers da Female Squad.

NSCDC ta yi magana yayin da ta tura jami'ai sama da 1800 zuwa jihar Kogi
NSCDC ta tura jami'ai 1,850 zuwa jihar Kogi domin ba da tsaro yayin bukukuwan Kirsimeti. Hoto: @official_NSCDC
Asali: Twitter

Hukumar NSCDC ta tsaurara tsaro a Kogi

Kwamandan NSCDC, Esther Akinlade, ta bayyana cewa, za a hada kai da sauran hukumomi don tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwa, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akinlade ta bayyana cewa jihar Kogi ta musamman ce saboda iyakarta da jihohi tara da kuma Abuja, wanda hakan ke kara bukatar tsauraran tsaro.

Ta yi kira ga matasa da su guji shiga duk wani aiki na rashin da’a ko aikata laifi da zai iya tada hankali a yayin bukukuwan Kirsimeti.

Jami'an NSCDC ta nemi hadin kan jama'ar Kogi

Kwamandan ta ce duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukuncin doka ba tare da nuna sassauci ba.

Akinlade ta bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa tare da bayar da bayanai kan duk wani aikin assha ga hukumomi.

Ta kara da cewa, wannan zai taimaka wajen kiyaye zaman lafiyar da jihar Kogi ke jin dadinsa a halin yanzu.

Bukukuwa 6 da za a yi a karshen shekara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya na tsumayin zuwan karshen shekarar 2024 domin gudanar da wasu manyan bukukuwa da aka saba duk shekara.

Kara karanta wannan

Kano: Gobara ta kone sashen gidan man NNPCL kurmus, an yi asara

A yayin da ake tunkarar karshen Disambar wannan shekarar, Legit Hausa ta tattaro muhimman bukukuwa 6 na karshen shekara da suka hada da bikin Kirsimeti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.