Rikicin Tafawa Balewa: Sarkin Musulmi Ya Bukaci Gwamna Ya Dakatar da Kafa Masarautar Sayawa

Rikicin Tafawa Balewa: Sarkin Musulmi Ya Bukaci Gwamna Ya Dakatar da Kafa Masarautar Sayawa

  • Majalisar Kolin Addinin Musulunci (NSCIA) ta bukaci gwamna Bala Muhammad ya dakatar da shirin kafa hedkwatar masarautar Sayawa a Tafawa Balewa
  • NSCIA ta bayyana cewa matakin kafa hedkwatar masarautar a garin ba zai tabbatar da zaman lafiya a yankin ba, kuma zai iya tada rikici a jihar
  • Sakataren NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dukkan kwamitocin da aka kafa a baya sun bayar da shawarar kafa hedkwatar masarautar a Bogoro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – Majalisar Kolin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta yi kira ga gwamnan Bauchi kan rikicin Tafawa Balewa.

A wata sanarwa da Sakatare-Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce wannan matakin zai iya kawo barazana ga zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

Bayan Naja'atu ta zargi Tinubu da ware Arewa, an dawo da Akanta Janar da aka sauke

Kauran Bauchi
NSCIA ta yi magana kan yunkurin kafa masarautar Sayawa a Tafawa Balewa. Hoto: Ibrahim Kaulaha MuhammaLawal Mu'azu Bauchi
Asali: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa NSCIA ta ce yunkurin kafa masarautar Sayawa a Tafawa Balewa ne tushen rikicin addini da kabilanci a yankin tun 1991.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin rikicin masarautar Sayawa

NSCIA ta bayyana cewa an samu matsaya tsakanin Majalisar Masarautar Bauchi da al’ummar Musulmi na Tafawa Balewa kan amincewa da kafa masarautar Sayawa domin zaman lafiya.

Sai NSCIA ta ce tun a wancan lokacin dukkanin bangarorin sun ki amincewa da kafa hedkwatar Sayawa da ke garin Tafawa Balewa.

Abin da ya faru a lokacin Isa Yuguda

Sanarwar NSCIA ta kara da cewa dukkan kwamitocin da gwamnonin baya suka kafa sun bayar da shawarar kafa hedkwatar masarautar a Bogoro.

NSCIA ta ce gwamna Isa Yuguda ya tura kudirin kafa masarautar zuwa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a shekarar 2014, inda ya bayyana Bogoro a matsayin hedkwatar.

Duk da haka, al’ummar Sayawa sun ki amincewa da masarautar idan ba za a kafa hedkwatarta a Tafawa Balewa ba.

Kara karanta wannan

ACHR: "Tinubu ya yi wani abin da tsofaffin shugabannin Najeriya suka gagara yi"

Kiran NSCIA ga gwamna Bala Muhammad

NSCIA ta nuna damuwa kan shirin gwamna Bala Muhammad na kafa hedkwatar masarautar a Tafawa Balewa, tana mai cewa wannan matakin bai dace ba.

Rahoton the Guardian ya nuna cewa NSCIA ta yi kira ga gwamnan da ya sake tunani kan tsarin tare da zaɓar wata hanya da za ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da hadin kai a yankin.

An bukaci gwamnati da ta tsaya kan shawarar kafa hedkwatar masarautar a Bogoro, kamar yadda dukkan kwamitoci suka bayar da shawara tun farko.

Gwamna yana gina makarantar Dahiru Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya fara gina makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Bauchi.

Gwamnatin Bauchi ta ce makarantar ce irinta ta farko a Arewa maso Gabas kuma an fitar da tsare tsare ta yadda makarantar za ta yi aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng