Kudurin Gyaran Haraji: Masani Ya Hango Babbar Matsala da Ke Tunkaro Najeriya

Kudurin Gyaran Haraji: Masani Ya Hango Babbar Matsala da Ke Tunkaro Najeriya

  • Wani masani kan haraji ya nuna damuwa kan kudirin gyaran haraji, yana mai cewa zai iya kawo barazana ga hadin kan kasa
  • Alhaji Shuaib Idris ya soki yadda aka tsara kudirin ba tare da shawarwari ba, yana mai ikirarin cewa an fifita wani yanki
  • Ba iya lalata hadin kai ba, masanin ya gargadi gwamnatin tarayya kan matsalolin da kudurin gyaran harajin zai haifar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Alhaji Shuaib Idris, wani kwararren akawu ya nuna damuwa kan kudirin gyaran haraji da ke gaban majalisar dokoki ta kasa.

Alhaji Idris ya yi gargadin cewa wannan gyaran haraji na iya kawo barazana ga hadin kan Najeriya idan ba a yi taka-tsan-tsan ba.

Alhaji Shuaib Idris ya yi magana kan kudurin gyuaran harajin Shugaba Bola Tinubu
Masani ya yi magana kan illolin da ke tattare da kudurin gyaran harajin Tinubu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Masani ya magantu kan kudurin gyaran haraji

Masanin ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Cibiyar Kasuwanci, Masana'antu, Ma'adinai da Noma ta Kaduna (KADCCIMA) ta shirya, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An taso shugaban kwamitin kudirin harajin Tinubu a gaba da zage zage

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Idris ya soki rashin cikakken shawara wajen tsara kudirin, yana mai cewa an fifita wani yankin maimakon a yi daidaito domin ci gaban kasa baki daya.

Ya nuna takaici kan yadda kudirin ya kai ga karatu na biyu a majalisar dokoki duk da kiraye-kirayen da al'umma ke yi na a sake duba lamarin.

"Matsalar da gyaran haraji za ta haifar" - Idris

Idris ya ce kudirin zai iya kara tsananta rikice-rikicen kasa, yake cewa kudirin ya yi kama da wanda zai haddasa rigimar yankuna.

Masanin ya ce:

“Wannan ba maganar Arewa da Kudu ba ce. Tambaya ita ce: ina adalci, gaskiya da nuna daidaito yake a nan?”

Ya kuma koka kan nauyin haraji da ya karu akan ‘yan Najeriya, musamman a lokaci da suke fama da cire tallafin mai da matsanancin talauci.

Ya bayyana cewa kashi 80% na ‘yan Najeriya na rayuwa a karkashin talauci, kuma karin haraji zai shafi masu amfani da kayayyaki ne kai tsaye.

Kara karanta wannan

Sanata Abdul Ningi ya buga muhawara da Akpabio a majalisar dattawa

Matasan Arewa na adawa da gyaran haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kungiyar matasan Arewa da ke jihar Taraba ta gargadi shugaba Bola Tinubu kan aiwatar da kudurin gyaran haraji.

Kungiyar ta yi zargin cewa kudurin gyaran harajin da ke gaban majalisar dokoki ta kasa zai tauye yankin Arewa ta fuskar tattalin arziki da rabon albarkatun kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.