An Taso Shugaban Kwamitin Kudirin Harajin Tinubu a Gaba da Zage Zage
- Shugaban kwamitin gyaran haraji na kasa, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa wasu ‘yan Najeriya suna zaginsa da iyalinsa
- Taiwo Oyedele ya ce duk da irin wannan kalubale, ba zai karaya ba wajen aiwatar da aikin gyaran tsarin haraji a Najeriya
- Hakan na zuwa ne yayin da wasu gwamnonin Arewa da shugabanni suka nuna rashin amincewa da kudirin gyara harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren Haraji na Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele ya bayyana yadda wasu ‘yan Najeriya ke zagin shi kan kudirin haraji.
Taiwo Oyedele ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da rahoton kwamitin ga kungiyar League of Northern Democrats (LND) a Abuja.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Oyedele ya yi bayani ne ga kungiyar LND game da kudirorin harajin da ake takaddama a kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu gudu babu ja da baya inji Oyedele
Taiwo Oyedele ya bayyana cewa duk da irin zagi da suke fitowa daga wasu ‘yan Najeriya, yana daukar wannan aiki a matsayin sadaukarwa ga al’umma.
“Ana zagin mu da iyalanmu a shafukan sada zumunta, amma mun kawar da kai.
Muna mayar da hankali a kan ko akwai abin da za mu dauka na gyara daga ra’ayoyin jama’a domin inganta aikace-aikacen mu,”
- Taiwo Oyedele
Ya kara da cewa dukkanin kudirorin gyaran haraji sun fito ne daga nazari da tattaunawa tsakanin kwamitin da ke dauke da wakilai daga sassa daban-daban na kasar.
Oyedele ya tabbatar da cewa babu wani shugaba ko kungiya kamar bankin duniya ko IMF da suka sanya su aiki sauya fasalin harajin.
Za ci gaba da tattauna kudirin haraji
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa za a cigaba da muhawara da karbar korafi da ya dace wajen inganta tsarin.
Ya kuma kara da cewa suna da wakilai a dukkan yankunan Najeriya da kuma ma'aikatu sama da 20 da suke tattaunawa a kan kudirin.
Tinubu ya sake magana kan kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada cewa kudirin harajin da ya aika ga majalisa zai amfani 'yan Najeriya.
An ruwaito cewa Bola Tinubu ya yi jawabin ne yayin wani taro a Ibadan inda ya ce bai kamata kudirin harajin ya jawo ce-ce-ku-ce ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng