‘Ka Na Kan Turba Mai Kyau’: Basarake a Arewa Ya Yabawa Salon Mulkin Tinubu

‘Ka Na Kan Turba Mai Kyau’: Basarake a Arewa Ya Yabawa Salon Mulkin Tinubu

  • Sarkin Gwandu da ke jihar Kebbi, Mai Martaba Muhammad Ilyasu Bashar ya kwarara yabo ga Shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa
  • Sarkin ya ce Bola Tinubu yana kan turba mai kyau musamman duba da kokarin da yake yi wurin samar da abubuwan more rayuwa
  • Basaraken ya kuma shawarci shugabanni da su kasance kusa da al'umma domin tabbatar da samun cigaba a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Sarkin Gwandu kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Kebbi, Mai Martaba Muhammad Ilyasu Bashar ya yabawa mulkin shugaban kasa, Bola Tinubu.

Basaraken ya yabawa Tinubu ne kan kokarinsa na ciyar da Najeriya gaba ta hanyar samar da muhimmiyar ababen more rayuwa.

Basarake a Arewa ya kwarara yabo ga Bola Tinubu
Sarkin Gwandu a jihar Kebbi ya yabawa salon mulkin Bola Tinubu. Hoto: Masarautar Gwandu.
Asali: Facebook

Sarkin Gwandu ya kora yabo ga Tinubu

Sarkin ya bayyana haka ne yayin karbar bakuncin Ministan ayyuka, Bello Muhammad Goronyo a daren jiya Laraba 18 ga watan Disambar 2024, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

'Ba ka da iko': Gwamnatin Tinubu ta soki gwamnan APC da Majalisa kan taba ciyamomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken yayin karbar bakuncin Ministan ya jaddada muhimmancin amana tsakanin shugabanni da kuma al’umma.

Ya bukaci 'yan Najeriya da su rika yarda da shugabanninsu domin tabbatar da alhakin mulki da kuma samar da nagartacciyar gwamnati da za ta tabbatar da ci gaba.

Basaraken ya shawarci shugabanni game da al'umma

"Shugabanni bai kamata su yi nesa da mabiyansu ba, musamman mazauna karkara domin tabbatar da cewa ayyukan da suke yi sun yi tasiri a rayuwarsu."

- Mai Martaba Muhammad Ilyasu Bashar

Ziyarar ta biyo bayan kaddamar da aikin titin Birnin Kebbi-Argungu a kan iyakar jihar Sokoto da aka gyara kwanan nan karkashin hukumar FERMA.

Sarkin ya bayyana shugabanci a matsayin nauyi mai girma tare da yabawa jajircewar gwamnatin wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Sarkin Gwandu ya ba yan siyasa shawara

Kun ji cewa Sarkin Gwandu, Abdullahi Bashar ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yi hakuri da juna yayin da zaben gwamnoni a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya tashi da jin labarin mutuwar yara 35, ya ba gwamna sabon umarni

Sarkin ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan siyasa su yi aiki domin kawar da duk wani kalubale da kasar nan ka iya fuskanta.

‘Yan takarar siyasa a jihar Kebbi sun ziyarci sarkin domin kwasar albarka daga hannunsa yayin da ake shirin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.