Sojoji Sun Cafke Masu Jigilar Makamai, Sun Kwato Tarin Albusurai

Sojoji Sun Cafke Masu Jigilar Makamai, Sun Kwato Tarin Albusurai

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro.sun yi nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zargi da jigilar makamai a jihar Bauchi
  • Sojojin na rundunar Operation Golden Peace sun cafke mutanen ne bayan sun kai wani samame cikin dare a gandun dajin Yankari na Bauchi
  • Jami'an tsaron sun ƙwato alburusai masu yawa a hannun waɗanda ake zargin yayin da suka tsare su domin ci gaba da gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Dakarun sojojin Najeriya na Operation Golden Peace, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da jigilar alburusai a jihar Bauchi.

Dakarun sojojin sun ƙwato alburusai masu yawa a samamen da suka kai a Kwari Biba, dake cikin gandun dajin Yankari a jihar Bauchi.

Sojoji sun kama masu laifi a Bauchi
Sojoji sun kama.masu jigilar makamai a Bauchi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

An cafke fitaccen mawakin siyasa a Kano, an zargi yan Kwankwasiyya da hannu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun cafke masu laifi a Bauchi

Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun kai samamen ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Laraba, 18 ga watan Disamban 2024.

A yayin samamen sun yi nasarar cafke wani mai suna Maikudi Danweri mai shekara 62 da Abubakar Hamza mai shekara 26.

Sojojin sun ƙwato harsashi guda 204 na musamman masu kaurin 7.62mm, babur, da kudi N10,000 daga hannun waɗanda ake zargin.

Waɗanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsu, suna wajen jami'an tsaro domin ci gaba da bincike.

Majiyar ta ci gaba da cewa, wannan farmakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na daƙile yaɗuwar makamai da alburusai a yankin.

Sojoji sun daƙile harin ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar MNJTF sun samu galaba kan ƴan ta'addan da suka farmaki sansaninsu a ƙasar Kamaru.

Sojojin na rundunar MNJTF sun samu nasarar daƙile harin da ƴan ta'addan suka kai da sanyin safiyar ranar Laraba, 18 ga watan Disamban 2024.

Ƙwararrun jami'an tsarom sun hallaka wasu daga cikin ƴan ta'addan bayan sun fatattake su daga sansanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng