Sanata a Arewa Ya Cika Alkawari, Ya Tura 'Ya 'Yan Talakawa 100 Karatu a Kasar Indiya
- Muhammad Salisu Gatawa ya ce bai taba tunanin yin karatu a kasar waje ba lokacin da sanatan shiyyarsu ya dauki nauyinsu
- Abubakar Isa ya ce bai yarda ya samu tallafin karatun ba har sai da aka sanar da cewa ya shirya zuwa Indiya domin yin karatu
- Senata Ibrahim Lamido ya tabbatar da cewa dalibai 100 daga Sokoto za su amfana da tallafin karatu na ƙasashen waje a bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Sanata Ibrahim Lamido zai dauki nauyin dalibai 100 domin su je kasashen waje su yi karatu a fannonin ilimi daban daban.
Muhammad Salisu Gatawa ɗaya daga cikin dalibai 57 daga jihar Sokoto da suka fara amfana da tallafin karatun ya ce bai taba sa ran zuwa waje karatu Indiya ba.

Asali: Facebook
Daliban sokoto sun yiwa sanata godiya
A wani rahoto na jaridar Daily Trust, Muhammad Gatawa ya ce ko a cikin mafarkinsa, bai taba tunanin zai je kasar waje yin karatu ba, amma Allah ya hukunta silar Sanata Ibrahi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammad Gatawa ya ce:
"Kamar a mafarki, yau ga mu a filin jirgin sama na Abuja za mu tafi Indiya don yin karatu. Alhamdulillah, haka Allah ya tsara."
Abubakar Isa, daya daga cikin daliban ya ce lokacin da aka karɓi takardunsa domin tura su zuwa kwamitin tantancewa, bai dauki hakan da muhimmanci ba.
Har sai bayan wasu 'yan kwanaki da aka kira shi domin ya je ayi masa gwaji, kuma daga baya aka sanar da shi cewa ya samu wannan tallafi na yin karatu a kasar waje.
Sanata ya fadi dalilin tura dalibai Indiya
A lokacin da yake bankwana da daliban kafin tafiyar su karatu zuwa Indiya a filin jirgin Nnamdi Azikiwe na Abuja, Senata Ibrahim Lamido ya yi wa daliban fatan alheri.

Kara karanta wannan
"Ku ƙara imani da Allah SWT," Gwamna ya yi magana bayan gobara ta laƙume miliyoyin Naira
Sanata Lamido ya bayyana cewa akalla dalibai 100 daga Sokoto za su amfana da wannan tallafin karatum na ƙasashen waje a wannan shekara.
Ya ce an riga da an samo gurbin karatu a jami'o'in Geeta da MJR a Indiya domin daliban suyi karatu a fannoni kamar lafiya, injiniyanci, da fasaha.
Dan majalisar Kano ya tura dalibai waje
A wani labarin, mun ruwaito cewa Hon. Abubakar Kabir, dan majalisar wakilai na mazabar Bichi daga jihar Kano, ya tura dalibai karatu kasar Malaysia.
Dan majalisar wakilan ya sanar da cewa dalibai 21 daga mazabarsa ta Bichi sun samu tallafin karatu na kasashen waje da ya yi alkawarin ba su.
Asali: Legit.ng