ACHR: "Tinubu Ya Yi Wani Abin da Tsofaffin Shugabannin Najeriya Suka Gagara Yi"

ACHR: "Tinubu Ya Yi Wani Abin da Tsofaffin Shugabannin Najeriya Suka Gagara Yi"

  • Kasafin kuɗin 2025 na Shugaba Bola Tinubu ya kai Naira tiriliyan 47.96, inda ya mayar da hankali kan gyara tattalin arziƙi
  • Cibiyar kare hakkin dan Adam ta Afrika (ACHR) ta ce kasafin da Tinubu ya gabatar shi ne mafi girma a tarihin Najeriya
  • ACHR ta yi imanin cewa kasafin 2025 zai rage hauhawar farashi, daidaita darajar Naira da kuma bunkasa al'ummar kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Cibiyar kare haƙƙin dan Adam ta Afrika (ACHR) ta bayyana kasafin kuɗin 2025 na Shugaba Bola Tinubu a matsayin mafi girma a tarihin Najeriya.

Kasafin, mai taken “Kasafin Warkarwa: Tsaron zaman lafiya, samar da ci gaba,” ya kai Naira tiriliyan 47.96, wanda ake gani zai magance manyan ƙalubale.

Cibiyar ACHR ta yi magana kan kasafin Naira tiriliyan 47.96 da Tinubu ya gabatar
Cibiyar ACHR ya yabawa Tinubu kan gabatar da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 47.96. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Cibiyar ACHR ta yabawa Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Kasafin 2025: Bayanai sun fara fitowa, Tinubu ya ware sama da N15bn don sayo motoci

Daraktan ACHR, Dakta Richard Ikani, ya bayyana cewa kasafin na 2025 ya nuna kyakkyawan tunani da hangen nesan Shugaba Tinubu, a cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Ikani ya ce babbar manufar kasafin ita ce dawo da kwanciyar hankali a tattalin arziƙi, musamman la’akari da matsalolin hauhawar farashi da karyewar darajar Naira.

Tattalin arziƙin Najeriya yana fama da hauhawar farashi wanda ya haura kashi 34%, inda kasafin ya yi niyyar rage hauhawar zuwa kashi 15% a 2025.

Kadan daga abin da kasafin 2025 ya kunsa

Shugaba Tinubu ya kuma mayar da hankali wajen daidaita darajar Naira, inda ake sa ran ta sauko daga N1,700 zuwa N1,500 a kasuwar hada-hadar duniya

Manazarta sun ce wannan matakin zai inganta tsarin kuɗin Najeriya, ƙarfafa amincewar masu zuba jari da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

Kasafin ya ƙuduri aniyar tara kuɗin shiga na Naira tiriliyan 34.82, wanda ke nufin ƙaruwar haraji da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Kara karanta wannan

Jerin muhimman ɓangarori 4 da Tinubu ya warewa kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2025

Fatan ACHR kan kasafin kudin 2025

A jawabin Tinubu, ya ce gwamnatin za ta samar da ganga miliyan 2.06 na danyen mai a kullum, tare da faɗaɗa haraji da inganta tattarawar kuɗin shiga a 2025.

Cibiyar ACHR ta ce wadannan matakan za su taimaka wajen rage dogaro da bashin ƙetare da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a ayyukan gwamnati.

Kasafin kuɗin na 2025, inji Dakta Ikani, zai sake maido da karfin tattalin arziƙin Najeriya, yayin da za a samu ci gaba mai dorewa a kowanne bangare.

Tinubu ta tono illar kasafin 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta fito ta nuna adawa da kasafin kudin Najeriya na 2025 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar a ranar Laraba.

Jam'iyyar PDP ta bukaci majalisar tarayya da ta yi fatali da wannan kasafin na Naira tiriliyan 47.96 da Tinubu ya gabatar gabanta kan zargin ba zai amfani talaka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.