Matatar Dangote Ta Yi Bayanin 'Rancen $1bn' da Kamfanin NNPCL Ya ba Ta

Matatar Dangote Ta Yi Bayanin 'Rancen $1bn' da Kamfanin NNPCL Ya ba Ta

  • Matatar Dangote ta yi martani ga labarin da ke nuna yadda ta samu rance daga NNPCL kafin ta fara aiki
  • Babban jami’in hulda da sadarwa na rukuni kamfanin Dangote, Anthony Chiejina ne ya yi bayani
  • Ya shawarci kamfanin mai na kasa a kan yadda zai rika fitar da bayanai don tabbatar da sahihi ne ya isa ga jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Matatar Dangote ta bayyana cewa hannun jarin kamfanin mai na Ƙasa (NNPCL) a matatar ya ragu daga 20% zuwa 7.24%.

Matatar ta bayyana cewa an samu raguwar hannun jarin sakamakon gazawar NNPCL wajen cika muhimman sharuddan hadin gwiwarsu.

NNPCL
Matatar Ɗangote ta musanta karbar rance daga NNPCL hoto: @DangoteGroup/NNPC Limited
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da babban jami’in hulda da sadarwa na rukuni kamfanin Dangote, Anthony Chiejina.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani a PDP, an kori mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi bayanin kudin NNPCL a matatar Dangote

Channels Television ta ruwaito matatar Dangote ta karyata labarin cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya ba shi rancen Dala biliyan daya.

Sanarwar matatar ta ce kudin hannun jari ne da aka sayarwa NNPCL wanda zai ba shi damar mallakar 20% a matatar.

Sanarwar Anthony Chiejina ta kara da cewa ;

“Muna da yarjejeniya kan sayar da 20% na hannun jarinmu a kan kimar Dala biliyan 2.76. Daga cikin wannan, mun amince za su biya Dala biliyan 1 kacal, yayin da sauran kudin za a biya su cikin shekaru biyar ta hanyar ragi daga man fetur da za su kawo mana da kuma daga ribarsu."

Matatar Dangote ta fadi gazawar NNPCL

Sanarwar da rukunin kamfanin Dangote ya fitar ta bayyana cewa gazawar NNPCL wajen samar da danyen mai ganga 300,000 a kowace rana kamar yadda aka amince

Kara karanta wannan

Kasafin kudi: Bola Tinubu ya sanya kowace Dala a kan N1500 a shekarar 2025

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan muhimmin bangare ne a yarjejeniyar, wanda ya jawo aka rage hannun jarin NNPCL daga 20% zuwa 7.24%. Matatar Dangote ta sake jaddada cewa tana mutunta matsayin NNPCL na abokin hulɗa mai muhimmanci, tare da neman a rika yada labarai na gaskiya.

NNPCL ya 'rantowa' matatar Dangote kudi

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya yi ikirarin ranto makudan Daloli domin taimaka wa matatar Dangote ta fara aikin tace danyen mai a Najeriya.

Shugaban watsa labaran kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, da ya fadi hakan yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Abuja ya ce gwamnati ta ranto Dala biliyan daya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.