Badakalar N110.4bn: Kotu Ta ba da Belin Yahaya Bello, Ta Gindaya Sharudda
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya samu beli a tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa kan baɗakalar N110.4bn
- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan a yayin zamanta na ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba
- Kotun ta ba da belin Yahaya Bello a kan kuɗi N500m tare da kawo mutum uku waɗanda za su tsaya masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan buƙatar Yahaya Bello ta neman a ba da belinsa.
Kotun ta bayar da belin tsohon gwamnan na jihar Kogi, kan Naira miliyan 500 da kuma mutum uku da za su tsaya masa.
Kotu ta ba da belin Yahaya Bello
Alƙalin kotun, mai shari’a MaryAnne Anenih ta bayyana hakan bayan sauraron sabuwar buƙatar belin da aka gabatar a gabanta ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun a zamanta na ƙarshe ta ƙi amincewa da buƙatar ba da belin tsohon gwamnan na jihar Kogi.
Yahaya Bello, tare da wasu mutane biyu, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu, suna fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC ke yi musu kan badaƙalar biliyan 110.4.
Sai dai, kotun ta bayar da belin waɗanda ake ƙara na biyu da na uku a kan kuɗi N300m tare da mutum biyu da za su tsaya musu da kuma wasu sharuɗɗan, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Wane sharaɗi kotu ta gindaya?
Da take karanto sharuɗɗan belin Yahaya Bello, alƙalin kotun ta ce dole ne waɗanda za su tsaya masa su kasance ƴan ƙasa nagari masu filaye a Abuja a cikin Maitama, Guzape, Apo, Wuse 2 ko Asokoro.
Ta ba da umarnin cewa waɗanda za su tsaya masa dole ne su ajiye takardun kadarorin a gaban magatakardar kotun, tare da hotunan fasfo guda biyu na kwanan nan.
"Wanda ake ƙara na farko ka da ya yi tafiya ba tare da izinin wannan kotu ba, kuma zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin."
- Mai shari'a MaryAnne Anenih
Yahaya Bello zai shigar da ƙara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan masu yaɗa labaran ƙarya a kansa.
Tsohon gwamnan ya yi barazanar ne bayan an yaɗa cewa yana caccakar shugaban ƙasa mai girma Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng