Halin Kunci: Dangote Ya Sake Tausayawa Al'umma, Ya Rage Farashin Mai a Najeriya

Halin Kunci: Dangote Ya Sake Tausayawa Al'umma, Ya Rage Farashin Mai a Najeriya

  • Duba da halin kunci da al'umma ke ciki musamman a wanna lokaci, Matatar Dangote ta sake rage farashin mai
  • Kamfanin ya dauki matakin ne duba da halin da ake ciki a Najeriya musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara
  • Wannan ba shi ne karon farko ba da kamfanin ke rage farashin saboda a watan Nuwambar 2024 ma ya rage zuwa N970

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Matatar mai na Aliko Dangote ta sake rage farashin man fetur a Najeriya yayin da aka fara bukukuwan karshen shekara.

Kamfanin ya rage farashin mai zuwa N899 kan kowace lita domin saukakawa al'umma a wannan lokaci.

Kamfanin Dangote ya rage farashin litar mai
Matatar man Aliko Dangote ta sake duba halin da ake ciki inda ta rage farashin litar mai. Hoto: Dangote Group.
Asali: UGC

Dangote ya sake rage farashin litar mai

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da daraktan hulda da jama'a, Anthony Chiejina ya fitar a yau Alhamis 19 ga watan Disambar 2024, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan kasuwa sun sanar da samun saukin farashin litar fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin taimakawa 'yan Najeriya da sauƙin wahala a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

“Matatar mai a Afirka ta farko ta Dangote wanda ta rage farashin mai zuwa N970 a kowace lita a ranar 24 ga Nuwamba."
"Yanzu ya sake sanar da sabon farashi na N899 a kowace lita."
"Wannan rangwamen an yi shi ne domin rage tsadar sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara da ake ciki.”

- Cewar sanarwar

Sauran tsare-tsare da kamfanin Dangote ya samar

Ya bayyana cewa matatar Dangote ta kuma ƙaddamar da hanyoyi da dama musamman domin ƙara amfanar al'umma.

“Don rage farashin sufuri a lokacin bukukuwan nan, Dangote ya bayar da rangwame kan farashin lita, Daga yau, man fetur ɗinmu zai kasance a kan farashin N899.50 kowace lita a wajen tashar lodin motoci."
"Haka kuma, ga kowane lita ɗaya da aka siya da kudi kai tsaye, masu amfani za su samu damar siyan karin lita ɗaya a kan bashin da ya samu goyon bayan bankuna kamar Access First Bank ko Zenith.”

Kara karanta wannan

Yadda NNPCL ya karbo rancen dala biliyan 1 domin tallafawa matatar man Dangote

- Anthony Chiejina

Matatar Dangote ta godewa yan Najeriya

Matatar ta nuna godiyarta ga 'yan Najeriya bisa goyon bayan da suke cigaba da bayarwa yayin da ƙasar ke shirin fara bukukuwan karshen shekara.

Chiejina ya kuma jaddada jajircewar matatar wajen tabbatar da cewa 'yan Najeriya na samun damar mallakar man fetur mai inganci, Punch ta ruwaito.

NNPCL ya karbi bashi domin tallafawa Dangote

Kun ji cewa, kamfanin NNPCL ya karbo bashin dala biliyan 1 domin tallafawa aikin matatar Dangote a lokacin da matatar ta shiga wata matsala.

An ruwaito cewa Mele Kyari ya jagoranci sauye-sauye a NNPCL, wanda ya kai ga samun riba a karon farko cikin shekaru masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.