Kashim Shettima Ya Kai Matsalolin Najeriya gaban Allah, Ya Yi Addu'ar Samun Ci Gaba
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya mika kuka ga Allah SWT a kan taimakon shugabannin Najeriya
- Ya yi addu'ar ne a lokacin da ya ke sauke faralin Umrah a Saudiyya a daidai lokacin da 'yan kasa ke kuka da matsin rayuwa
- Kashim Shettima ya yi addu'ar shugabanni za su yi koyi da halayen fiyayyen halitta SAW wajen adalci ga mazauna kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Saudiyya - Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yi addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Najeriya yayin aikin Umarah. Mataimakin shugaban kasar sa ya roki Allah SWT ya azurta shugabannin da jagoranci na gari tare da jagorancin al’ummar kasa da gaskiya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Mataimakin Shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar a shafinsa na X.
Kashim Shettima yana yi wa Najeriya addu’a
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya nemi Allah SWT ya taimaki shugabannin kasar nan don sauke nauyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar da hadiminsa ya bayar:
"Allah ya ba shugabanninmu, daga Shugaban Kasa har zuwa kansilolinmu a matakin ƙananan hukumomi, hikima, haƙuri, da kyautatawa irin na Annabi Muhammad (SAW) a cikin duk al’amuransu."
"Allah ya ba mu hikimar shugabanci mai kyau domin gudanar da harkokin kasarmu yadda ya dace kuma mu yi wa al’umma hidima cikin adalci."
An dage ganawar Kashim Shettima da shugaban IsDB
An dage tattaunawa tsakanin Kashim Shettima da shugaban bankin raya kasashen Musulunci (IsDB) a Jeddah zuwa wata rana ta daban.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai kammala ayyukansa, sannan ya juyi zuwa gida Najeriya gobe, Juma'a.
Kashim Shettima ya sauka a Saudiyya
A baya, kun ji cewa mataimakin shugaban kasar nan, Sanata Kashim Shettima ya sauka a kasa mai tsarki bayan kammala ziyarar aiki a Dubai, hadaddiyar daular Larabawa.
Kafin a soke ganawar, an sa ran mataimakin Bola Tinubu zai gana da shugaban bankin raya kasashen Musulunci domin ci gaba da gudanar da shirinsa na noma a fadin kasar.
Asali: Legit.ng