Tinubu: PDP Ta Tono 'Illolin' da ke cikin Kasafin 2025, Ta Gargadi Majalisa

Tinubu: PDP Ta Tono 'Illolin' da ke cikin Kasafin 2025, Ta Gargadi Majalisa

  • PDP ta bayyana kasafin kudin 2025 da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar a matsayin wanda ba zai amfani talakawa ba
  • Jam'iyyar ta bukaci Majalisar Tarayya ta yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta domin sake fasalin kasafin kudin
  • PDP ta ce kasafin kudin ya gaza samar da hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki, tsaro, da walwalar 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci Majalisar Tarayya da kada ta amince da kasafin kudin 2025 da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar.

PDP ta bayyana cewa kasafin kudin ya gaza samar da matakan da za su bunkasa tattalin arziki da rage radadin talauci da ake fama da shi a kasar.

Kara karanta wannan

Barkwancin Tinubu yayin gabatar da kasafin 2025 ya jawo ihu a majalisa

Kasafin kudi
PDP ta bukaci kin amincewa da kasafin 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Getty Images

Jaridar the Cable ta rahoto cewa kakakin jam'iyyar PDP, Debo Ologunagba ne ya fitar da sanarwar bayan Bola Tinubu ya gabatar da kasafin a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta caccaki kasafin kudin 2025

Cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ya fitar, jam’iyyar ta ce kasafin kudin da Tinubu ya gabatar ya yi kama da jawabin yakin neman zabe.

A cewar PDP, kasafin bai yi wani muhimmin tanadi ga bangarorin tattalin arzikin da ke da mahimmanci ba.

Arise News ya rahoto cewa jam'iyyar ta bayyana ikirarin shugaban kasa kan farfado da tattalin arziki a matsayin zancen gizo da koki.

PDP ta yi kira ga majalisa kan kasafin 2025

Jam'iyyar PDP ta yi kira ga Majalisar Tarayya da ta yi amfani da ikon da sashe na 80, 81, da 82 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ta domin sake fasalin kasafin kudin.

Kara karanta wannan

Sanata Abdul Ningi ya buga muhawara da Akpabio a majalisar dattawa

A cikin sanarwar, PDP ta ce:

“Ya kamata majalisar ta samar da tsare-tsaren kasafin kudi da suka dace, wadanda za su taimaka wajen farfado da tattalin arziki, bunkasa masana’antu, rage tsadar kayan masarufi, da tabbatar da walwala ga ‘yan Najeriya.”

- Debo Ologunagba

Hakazalika, jam'iyyar ta bayyana cewa kasafin kudin bai tanadi hanyoyin magance matsalolin tsaro, rage tsadar kayayyaki kamar man fetur, abinci, da wutar lantarki ba.

Tinubu ya tayar da hargitsi a majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya yi maganar da ta jawo hargitsi a majalisa yayin gabatar da kasafin kudin 2025.

Shugaba Bola Tinubu ya yi barkwanci a majalisar tarayya inda ya ce dukkan 'yan majalisa sun samu tazarce a zaben 2027 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng