Jerin Muhimman Ɓangarorin da Tinubu Ya Warewa Kaso Mafi Tsoka a Kasafin Kudin 2025

Jerin Muhimman Ɓangarorin da Tinubu Ya Warewa Kaso Mafi Tsoka a Kasafin Kudin 2025

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a zaman haɗin guiwa na Majalisar Tarayya ta 10
  • Kasafin kuɗin wanda aka yi ƙiyasin zai laƙume kuɗi Naira tiriliyan 47.96 ya warewa wasu muhimman ɓangarori kuɗi masu tsoka
  • Batun tsaron ƴan Najeriya shi ne na farko wanda zai laƙume Naira tiriliyan 4.91, sai kuma gina ababen more rayuwa, ilimi da kuma lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kuɗin 2025 a zaman haɗin guiwa na Majalisar Tarayya ta 10 ranar Laraba.

Shugaba Tinubu ya yi wa kasafin taken, "kasafin kuɗin gyara ƙasa: samar da tsaro da wadata."

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bangarorin da aka warewa kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2025 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya wallafa cikakkken jawabin da ya yi yayin gabatar da kasafin 2025 wanda zai laƙume Naira tiriliyan 47.96 a shafinsa na manhajar X.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kasafin kudin na ɗaya daga cikin haƙƙoƙin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ɗora masa.

Batun tsaro zai fi lakume kuɗi a 2025

Duk da shugaban ƙasa bai bayyana adadin kuɗin da aka warewa kowane ɓangare ba, amma ya jero muhimman wuraren da suka fi samun kaso mai tsoka.

Batun tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya shi ne na farko, inda Shugaba Tinubu ya ce zai laƙume Naira tiriliyan 4.91 a 2025.

Sai kuma ɓangaren samar da ababen more rayuwa wanda zai ci Naira tiriliyan 4.06, ilimi kuma Naira tiriiyan 3.52 da ɓangaren lafiya da zai laƙume Naira tiriliyan 2.48.

Jerin ɓangarorin da suka samu kaso mai tsoka

S/NƁangareKasafin 2025
1TsaroN4.91trn
2Ababen more rayuwaN4.06trn
3IlimiN3.52trn
4LafiyaN2.48trn

Bola Tinubu ya tafi hutu Legas

A wani rahoton, an ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tafi mahaifarsa jihar Legas domin yin hutun kirismeti da sabuwar shekara a gida.

A mako mai zuwa ake sa rana gwamnatin tarayya za ta ba da hutun bukukuwan kirismeti ta bana 2024 da kuma hutun sabuwar shekara da zai biyo baya a 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262