Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutu bayan Gabatar da Kasafin Kudin 2025

Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutu bayan Gabatar da Kasafin Kudin 2025

  • Shugaban ƙasan Najeriya ya tafi hutun bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara a jiharsa ta Legas da ke yankin Kudu maso Yamma
  • Mai girma Bola Tinubu ya isa Legas ne da rana jim kaɗan bayan ya kammala gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a gaban majalisar tarayya
  • Bayan isarsa filin jirgin saman Murtala Muhammad, ya samu tarba daga wajen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu da sauran ƙusoshin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaba Bola Tinubu ya isa jihar Legas domin hutun bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Shugaba Tinubu ya isa filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas, da misalin ƙarfe 3:23 na rana a ranar Laraba.

Shugaba Tinubu ya tafi hutu a Legas
Shugaba Tinubu ya tafi hutun Kirsimeti a Legas Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Cikakken jawabin Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudin 2025 a Majalisar Tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dada Olusegun ya sanya bidiyon tarbar da aka yi wa Shugaba Tinubu a filin jirgin saman Murtala Muhammad a shafinsa na X.

Kafin ya bar Abuja, shugaban ƙasan ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2025 ga majalisar tarayya domin tantancewa tare da amincewa da shi.

Tinubu ya isa Legas domin hutu

Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya samu tarba daga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, mataimakin gwamna Obafemi Hamzat da ƙusoshin gwamnati a filin jirgin.

"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa jihar Legas domin gudanar da hutun bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara."

"Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, mataimakin gwamna, Obafemi Hamzat, da mambobin majalisar zartarwa sun tarbi shugaban ƙasan a filin jirgin saman Murtala Mohammed."

"Kafin ya tafi Legas, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2025, wanda ya kai N47.9trn, a gaban wani taron haɗin gwiwa na majalisar tarayya a Abuja."

Kara karanta wannan

Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025, ya fadi yadda za a kashe tiriliyoyi

- Bayo Onanuga

Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasan Najeriya, mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya gabatarwa majalisar tarayya kasafin kuɗin shekarar 2025.

Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin ne a gaban ƴan majalisar tarayya a ranar Laraba, 18 ga watan Disamban 2024..

Tinubu ya yi bayanin yadda za a kashe kuɗaɗen da ke cikin kasafin kuɗin na shekarar 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng