Kasafin Kudi: Bola Tinubu Ya Sanya Kowace Dala a kan N1500 a Shekarar 2025

Kasafin Kudi: Bola Tinubu Ya Sanya Kowace Dala a kan N1500 a Shekarar 2025

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 wanda ya kara darajar Naira fiye da da
  • Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a gaban majalisar hadin gwiwa a ranar Laraba inda ya sanya kowace Dala kan N1500
  • Wannan na nufin takardar kudin Najeriya ta kara samun daraja da N200 a kan yadda aka sa a baya bisa wasu dalilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanya farashin kowace Dala a kan N1,500 a ksafin kudin 2025. A ranar Laraba 18 Disamba, 2024 ne Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin a zaman hadin gwiwa na Majalisar Tarayya ta 10.

Tinubu
An daga darajar Naira da N200 Hoto: Bayo Onanuga/Hussein Faleh
Asali: Facebook

Channels Television ta ruwaito Tinubu na cewa hakan zai ba gwamnati damar tabbatar da aiwatar da kasafin kudin na 2025 ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Kasafin 2025: Bayanai sun fara fitowa, Tinubu ya ware sama da N15bn don sayo motoci

Tinubu ya daga darajar Naira a kasafin 2025

Ripples Nigeria ta ruwaito cewa kasafin kudin 2025 ya nuna cewa darajar Dala ta ragu da kimanin N200 daga farashin N1,700 a baya. Shugaba Tinubu ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kasafin kudin na hasashen cewa hauhawar farashin kaya zai ragu daga 34.6% zuwa 15% a shekara mai zuwa, yayin da tsarin musayar kudade zai inganta daga kusan N1,700 kan Dala zuwa N1,500.

Ana sa ran samar da danyen mai na yau da kullum zai kai ganga miliyan 2.06, kamar yadda kasafin ya nuna.

Dalilin Tinubu sanya darajar N1500

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ana sa ran samun dagawar darajar Naira ne saboda wasu dalilan. Daga cikin abubuwan da ya jero akwai rage shigo da man fetur daga kasashen waje da karuwar fitar da kayayyakin mai da aka tace.

Sauran dalilan sun hada da samun yabanya mai kyau saboda karuwar ingancin tsaro a sassan kasar nan, kamar yadda shugaban ya ce.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan da yamata ku sani game da kasafin kudin 2025

Tinubu ya gabatar da kasafin kudi

A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a gaban zaman majalisa na hadin gwiwa inda ya gabatar da kasafin shekarar 2025 a ranar Laraba.

Tinubu ya isa harabar majalisar ne da misalin karfe 12:10 na rana tare da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.