'Ka Yi Hattara': Akpabio Ya Gano Ministocin da ba Su Dace da Gwamnatin Tinubu ba

'Ka Yi Hattara': Akpabio Ya Gano Ministocin da ba Su Dace da Gwamnatin Tinubu ba

  • Sanata Godswill Akpabio ya ce ministoci masu bijirewa gayyatar Majalisa ba su da gurbi a cikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Shugaban majalisar dattawan ya gargadi ministoci yana mai jaddada cewa majalisa na da hurumin gayyatarsu duk lokacin da ta so
  • Akpabio ya yi wannan maganar ne lokacin da Tinubu ya gabatar da kasafin N47.9trn a gaban majalisar tarayya a ranar Laraba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gargadi wasu daga cikin 'yan majalisar ministocinsa.

Sanata Akpabio ya yi ikirarin cewa akwai wasu ministoci a gwamnatin Tinubu da ke bijirewa umarnin majalisar tarayya idan ta bukaci ganinsu.

Sanata Akpabio ya yi magana kan ministoci yayin da Tinubu ya gabatar da kasafin 2025
Sanata Akpabio ya fadawa Tinubu wasu ministoci da ba su dace da gwamnatinsa ba. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shugaban majalisar dattawan fadawa Tinubu da ya yi hattara da ire iren waɗannan ministocin domin ba su cancanci zama cikin gwamnatinsa ba, a cewar rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Sanata Abdul Ningi ya buga muhawara da Akpabio a majalisar dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya gano ministoci masu taurin kai

Shugaban Majalisar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na 2025 a gaban majalisar dokokin tarayya.

"Wadanda suka yi watsi da gayyatar da majalisar dokoki ta yi masu ba masu kishin dimokuradiyya ba ne don haka ba su da matsugunni a cikin gwamnatinka."

- A cewar Sanata Akpabio.

Sanata Akpabio ya ce ministoci da manyan jami’an gwamnati su na da alhakin amsa gayyatar majalisa don bayar da bayanai kan ayyukansu.

Tinubu ya gabatar da kasafin 2025

Ya ja hankalin ministoci cewa majalisa na da ikon daukar mataki idan har suka ki mata taurin kai na kin amsa gayyatar 'yan majalisar dattawa ko wakilai.

An ce Shugaba Tinubu ya samu rakiyar SGF, George Akume da shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila, lokacin gabatar da kasafin kuɗin.

Kasafin kuɗin na 2025, mai darajar Naira tiriliyan 47.9, ya kunshi manyan shirye-shirye na ci gaban tattalin arziki da bunkasa al’umma.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dura kan Tinubu, ya ce ba zai yi aiki da tsare tsaren 'T Pain' ba

An tsaurara tsaro a majalisar tarayya

A wani labarin, mun ruwaito cewa an tsaurara matakan tsaro a zaurwn majalisar tarayya yayin da Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.

An ce an jibge ‘yan sanda dauke da makamai a manyan kofofin shiga cikin farfajiyar majalisar kuma an tsaurara binciken mutane da ababen hawa da ke kai komo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.