Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kudin 2025, Ya Fadi Yadda Za a Kashe Kudaden
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubuya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ga ƴan majalisar tarayya a birnin Abuja
- Mai girma Bola Tinubu ya yi jawabin yadda za a kashe kuɗaɗen da ke cikin kasafin kuɗin na 2025
- A jawabin da shugaban ƙasan ya yi ya ce an ware Naira tiriliyan 15.81 domin biyan basussukan da gwamnati ta ciyo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 a gaban ƴan majalisar tarayya.
Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin ne a ranar Laraba, 18 ga watan Disamban 2024.
Shugaban ƙasan ya sanya jawabin da ya yi wajen gabatar da kasafin kuɗin a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Tinubu zai kashe kuɗaɗen
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an ware Naira Tiriliyan 15.81 domin biyan basussuka a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025
Tsaro ne ke kan gaba wajen samun kaso mai tsoka a cikin kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 47.9 da shugaban ƙasan ya gabatar.
Ya bayyana cewa an warewa tsaro Naira tiriliyan 4.91, kiwon lafiya Naira tiriliyan 4.06, ababen more rayuwa Naira tiriliyan 2.4 yayin da ɓangaren ilmi ya samu Naira tiriliyan 3.5.
Tinubu ya ce a cikin kasafin kuɗin an yi hasashen samun kuɗaɗen shiga Naira tiriliyan 34.8.
Biyan basussuka zai laƙume N15trn
Shugaban ƙasan ya ƙara da cewa daga cikin kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 47.90, an ware Naira tiriliyan 15.81 domin biyan basussuka tare da giɓin Naira tiriliyan 13.0.
Ya kuma ƙara da cewa, an yi hasashen hauhawar farashin kayayyaki zai ragu daga kaso 34.3% zuwa kaso 15% yayin da aka rage farashin Dala daga N1700/$ zuwa N1400/$.
An tsauraro a majalisa saboda zuwan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa an tsaurara tsaro a majalisar tarayya yayin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke shirin gabatar da kasafin kuɗin 2025.
Shugaban ƙasan ya shirya gabatar da kasafin ne a wani zaman haɗin gwiwa tsakanin ƴan majalisar wakilai da na dattawa a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng