Gwamnatin Abba Ta Gindaya Sharadin Kwace Wasu Filaye a Jihar Kano

Gwamnatin Abba Ta Gindaya Sharadin Kwace Wasu Filaye a Jihar Kano

  • Gwamnatin Kano ta sanar da wa'adin sabunta takardun filaye da sauran kadarori domin gujewa rasa su a jihar
  • Kwamishinan kasa da tsare tsare, Abduljabbar Umar ne ya sanar da matakin a hira da ya yi da manema labarai a ranar Laraba
  • Ya bayyana cewa duk wanda aka samu da kin bin umarnin zai iya rasa filinsa bayan ranar 31 ga watan Janairu, 2025

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta gargadi duk masu filaye a jihar da su sabunta takardun mallakar filayensu a cikin gaggawa.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gargadi cewa duk wanda ya ki sabunta takardunsa zai iya rasa filayensa ko kadarar da ya mallaka.

Gwamna
Gwamnatin Kano ta ba da wa'adin sabunta takardun filaye Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kwamishinan kasa da tsare tsare, Abduljabbar Umar, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gwangwaje malamar da ta mayar da kudin gwamnati N748,320

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bada wa’adin sabunta takardun fili a Kano

Jaridar Guardian ta wallafa cewa gwamnatin Kano ta bayar da wa’adin kwanaki 44 ga duk masu filaye su sabunta takardun mallakar kadarorinsu.

Ya kara da cewa duk takardun mallakar filaye za su zama marasa amfani idan wa’adin ranar 31 ga Janairu, 2025 ya cika.

Kano: Dalilin neman sabunta takardun filaye

Gwamna Abba Kabir Yusuf, a ranar 25 ga Nuwamba, 2024, ya kaddamar da tsarin sabunta takardun mallakar filaye a jihar domin samar da tsarin filaye da gaskiya.

Abduljabbar Umar, ya ce:

“Ina so in tunatar da jama’a cewa, a kokarin wannan gwamnati na samar da hanya mai inganci da sauki don samun takardun mallakar filaye, tare da tabbatar da kariya da karfafa ikon mallakar filaye a jihar, an samar da sabbin kayayyakin zamani a hukumar tsarin bayanan filaye ta Kano (KANGIS).”

An tantance sababbin kwamishinoni a Kano

A baya mun ruwaito cewa majalisar dokokin Kano ta amince da nadin mutane bakwai a matsayin kwamishinoni a bangarori daban daban kamar yadda gwamna ya nema.

Kara karanta wannan

Saratu Daso, El Muaz da wasu 'yan wasan Kannywood 2 da suka rasu a 2024

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya aika da sunayen Shehu Wada Sagagi, Abdulkadir Abdulsalam, Gaddafi Sani Shehu, Ibrahim Wayya, Dr. Dahiru Hashim Muhammad zuwa majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.