"Abin da Ya Sa Wike Ya Sauke 'Dan Arewa daga Mukamin Shugaban Ma'aikatar Raya Abuja"
- Majiyoyi sun shaida cewa ministan Abuja, ya dakatar da Injiniya Shehu Ahmad Hadi daga shugaban FCDA saboda samun sabani
- Wani jami’i a FCDA ya ce Hadi na bayar da shawarwari kan ayyuka da kwangiloli da suka saba da ra'ayin mai gidansa, Nyesom Wike
- A yayin da majiyoyin suka yi karin bayani, ofishin Wike bai bayyana dalili ko kuma lokacin da dakatarwar za ta kare ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan FCT, Nyesom Wike, ya dakatar da Injiniya Shehu Ahmad Hadi daga mukaminsa na babban sakataren ma'aikatar raya Abuja (FCDA).
An dakatar da Hadi ne a ranar 14 ga Nuwamba, ba tare da wani bayani kan dalilin korar ba, kuma aka umurce shi da ya mika mulki ga wani darakta.

Source: Twitter
Dalilin Nyesom Wike na korar shugaban FCDA
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Hadi ya kasance yana tsaurara ra'ayi kan yadda za a gudanar da ayyuka da kwangiloli, abin da ya haifar masa da matsaloli.
Wani babban jami’in FCTA ya bayyana cewa ra'ayin Hadi game da yadda za a aiwatar da ayyuka bai yi wa wasu dadi ba, musamman Nyesom Wike.
An bayyana cewa Hadi yana bayar da shawara kan hanyoyin da ya dace a bi wajen bayar da kwangila da aiwatar da ayyuka, da ya saba da ra'ayin ministan Abuja.
Injiniya Hadi bai ce komai kan korarsa ba
Wani ma’aikacin FCDA ya ce shawarwarin Hadi kan wasu ayyuka ya saba da tsarin da ministan yake so, wanda hakan ya sa aka dakatar da shi.
Duk da haka, Hadi bai bayyana wani ra’ayi kan dakatarwar ba, kuma bai amsa kiran waya ko sakonni da aka tura masa ba.
Wasu daga cikin mutanen da aka sani suna da kusanci da shi sun ki yin tsokaci kan batun.
Wike bai bayyana dalilin korar Hadi ba
Amma mai magana da yawun ministan, Lere Olayinka, ya ce dakatarwar da aka yi wa Hadi za ta ci gaba da kasancewa har sai Wike ya bayar da sabon umarni.
Da aka tambaye shi dalilin dakatarwar da ministan ya yi wa Hadi, Mista Lere ya bayyana cewa ba zai iya bayyana dalilin ba a halin yanzu.
Richard Yunana Dauda, daraktan sashen Injiniyanci na ma'aikatar FCDA, ya karɓi ragamar mukamin babban sakatare na rikon kwarya bayan tafiyar Hadi.
Wike zai biya diyyar rusa masallacin Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa Minista Nyesom Wike ya ba hukumar raya Abuja (FCDA) umarnin nemo tsarin da za a bi wajen biyan diyyar rusa masallacin Abuja.
Wike ya umarci shugaban hukumar FCDA, Injiniya Shehu Ahmad Hadi ya gaggauta kawo masa rahoton tsarin cikin awa 78 domin magance ce-ce-ku-cen da ake yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

