Gwamnati Ta Gwangwaje Malamar da Ta Mayar da Kudin Gwamnati N748,320

Gwamnati Ta Gwangwaje Malamar da Ta Mayar da Kudin Gwamnati N748,320

  • Gwamnatin Katsina ta karrama Malamar makaranta, Abdulkadir-Yanmama da N500,000 bayan ta mayar da N748,320
  • An aika wa malamar kudin ne bisa kuskure daga cikin shirin ciyar da 'yan makarantun firamare na gwamnatin tarayya
  • Bayan malamar ta ga shigowar kudin ne ta garzaya wajen mahukunta domin sanar da su cewa babu ita a tsarin dafa abincin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Amana ta yi wa wata malamar makaranta a Katsina rana bayan ta mayar da naira N748,320 da gwamnati ta aika mata bisa kuskure.

Lamarin ya faranta ran gwamnatin jihar Katsina, har ta karrama Malama Abdulkadir-Yanmama da kyautar N500,000 a ranar Talata.

Katsina
Gwamnati ta karrama malamar makaranta a Katsina Hoto: @abdullahayofel
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa an kudin da aka aikawa malamar na daga cikin shirin ciyar da daliban firamare na gwamnatin tarayya a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta gindaya sharadin kwace wasu filaye a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta karrama malamar makaranta

Jaridar People’s Gazette ta ruwaito cewa daraktan hukumar zuba jari na al’umma ta Katsina, Dr. Mudassir Nasir, ne ya mika kyautar ga kudin ga malamar.

Nasir ya bayyana cewa;

“Ta shaida mana cewa ta samu saƙon kudi daga banki mai taken biyan dillalai masu samar da abinci kyauta ga ɗaliban makarantu.
“Matar ta yanke shawarar zuwa ofishinmu domin ba ta cikin jerin dillalan da ke samar da abinci ga ɗalibanmu, kuma ba ta da wata alaƙa da irin wannan shirin.

Gwamnatin Katsina ta yabi malamar makaranta

Dr. Mudassir Nasir ya bayyana cewa amana da matar ta nuna ya sanya gwamnan Katsina, Umaru Dikko Radda ya ji dadin gaskiyar da ta nuna.

Gwamna Umaru Dikko Radda ya kuma umarci sauran mazauna jihar da su yi koyi da kyakkyawan halin da malamar makarantar ta nuna.

Gwamnatin Katsina za ta raba tallafin N3.9bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Katsina ta fara shirin raba tallafin kudi da yawansa ya kai Naira biliyan 3.9 domin tallafawa mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun shiga alhini, sun yi ta'aziyyar mutuwar mutane a hadarin jirgin Binuwai

Za a raba tallafi a yankuna 65, manoma 19,068, da kananan 'yan kasuwa 4,095 domin bunkasa tattalin arzikin jihar a shirin ya tallafa wa mutane sama da miliyan 1.9.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.