'Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ta Kashe Jaririnta, Ta Fadi Dalili

'Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ta Kashe Jaririnta, Ta Fadi Dalili

  • Wata budurwa a jihar Delta ta gaji da jin zagin mutane inda ta ɗauki matakin aikata ɗanyen aiki kan jaririn da ta tsugunna ta haifa
  • Budurwar dai ta kashe jaririn ta hanyar jefa shi a cikin rafi bayan mutane sun dame ta da surutun cewa ba shi da uba
  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Delta sun cafke budurwar wacce ta nuna nadama kan mummunan aikin da ta aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Jami'an ƴan sanda a jihar Delta sun cafke wata budurwa zargin kashe jaririnta mai watanni 10 a duniya.

Ƴan sandan sun cafke budurwar ne wacce ake zargi da hallaka jaririn ta hanyar jefa shi cikin rafi, bayan tun da farko ta ce yaron ya ɓace.

Budurwa ta kashe jaririnta a Delta
'Yan sanda sun kama budurwa kan kisan danta a Delta Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan sanda sun kama masu laifi a Delta

Tashar Channels tv ta rahoto cewa an tasa ƙeyar wacce ake zargin ne a hedkwatar ƴan sandan jihar da ke Asaba, babban birnin jihar Delta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dauki mataki bayan an yi musu tayin cin hancin N66m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tare da ita akwai wani mutum da ake zargin ya yaudari wani yaro ɗan shekara takwas zuwa wajen wani boka.

Daga baya an kashe yaron, sannan bokan ya yi amfani da sassan jikinsa wajen yin tsafi.

Meyasa ta kashe jaririn?

Wacce ake zargin, ta amsa laifin ta, inda ta bayyana cewa ta kashe yaron nata ne saboda surutun da ake yi mata bayan mahaifinsa ya ce ba ɗansa ba ne.

Matashiyar da ake zargi da kashe jaririnta ta ƙara da cewa ta aikata ɗanyen aikin ne saboda karan tsana da mutane suka ɗora mata.

Ta amince da aikata laifin kuma ta nuna nadamarta kan bin da ta aikata.

Ƴan sanda sun cafke manyan ƴan daba

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan Kano sun tashi tsaye domin yaƙi da matsalar ƴan daba a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Kotu ta zauna kan shari'ar 'yan boko haram, miyagu 325 sun san makomarsu

Ƴan sandan sun gudanar da wani samame a wasu unguwannin birnin Kano da nufin cafke matasan da ke da hannu a ayyukan daba.

Kakakin ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an cafke manyan ƴan daba tare da ƙwato makamai a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng