Garkuwa da Mutane: Yadda Aka Ba 'Yan Bindiga Kudin Fansar Naira Tiriliyan 2.2 a Shekara

Garkuwa da Mutane: Yadda Aka Ba 'Yan Bindiga Kudin Fansar Naira Tiriliyan 2.2 a Shekara

  • Rahoton Cibiyar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna an kashe mutane 614,937 yayin da aka yi garkuwa da 2,235,954 a shekara daya
  • NBS ta ce yankin Arewa maso Yamma ya fi samun yawan garkuwa da mutane da kuma biyan kudin fansa da ya kai Naira tiriliyan
  • A cewar rahoton, kaso 91% na garkuwa da mutanen an yi sa ne domin neman kudin fansa daga wajen wadanda aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - Cibiyar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da sabon rahoto da ya bayyana irin yadda garkuwa da mutane da kashe-kashe suka addabi Najeriya.

A rahoton, an bayyana cewa mutane 614,937 ne aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da 2,235,954 a fadin kasar daga Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.

Kara karanta wannan

Matakan da gwamnonin Arewa suka hadu suka dauka na murkushe 'yan bindiga

Turji
Rahoton garkuwa da mutane na shekara 1 a Najeriya. Hoto: Nigerian Police Force|Adamu Muhammad
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa jimillar kudin fansa da aka biya ya kai Naira tiriliyan N2.3, wanda ke nuni da matsanancin barazanar tsaro a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garkuwa da mutane a birane da kauyuka

Rahoton ya nuna cewa an fi samun kashe-kashe a yankunan karkara inda aka samu rahotanni 335,827, yayin da a birane aka samu 279,110.

Yankin Arewa maso Yamma ne ya fi samun yawan kashe-kashe (206,030), sai Arewa maso Gabas (188,992), yayin da yankin Kudu maso Yamma ya fi karanci da rahotanni 15,693.

Adadin mutanen da aka sace a shekara 1

A bangaren garkuwa da mutane, an bayyana cewa mutane 1,668,104 ne aka yi garkuwa da su a karkara, yayin da aka yi garkuwa da 567,850 a birane.

Arewa maso Yamma ne ya fi samun garkuwa da mutane, inda aka sace mutane 1,420,307, sai Arewa ta Tsakiya 317,837 da Kudu maso Gabas 110,432

Kara karanta wannan

CBN ya kayyade kudin da 'yan Najeriya za su rika cirewa daga masu POS

Kudin fansa da aka biya a Najeriya

The Cable ta wallafa cewa rahoton ya nuna cewa kaso 82.1% cikin wadanda aka yi garkuwa da su an sako su, yayin da kaso 12.8% aka kashe su, sai kuma kaso 3.3% har yanzu suna tsare.

Sarkin Gobir
Mai martaba Sarkin Gobir da masu garkuwa suka kashe a Arewa ta Yamma. Hoto: Ibrahim Muhammad
Asali: Facebook

Fiye da Naira tiriliyan 2.2 aka biya a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a Najeriya tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024:

  • Arewa ta Yamma: Naira tiriliyan 1.17
  • Arewa ta Tsakiya: Naira biliyan 469.74
  • Kudu maso Yamma: Naira biliyan 248.78
  • Arewa maso Gabas: Naira biliyan 166.14
  • Kudu maso Kudu: Naira biliyan 90.05
  • Kudu maso Gabas Naira biliyan 85.44

Dalilan garkuwa da mutane a Najeriya

Rahoton ya ce kaso 91% na garkuwa da mutanen na neman kudin fansa ne, yayin da kaso 2.4% suka danganci manufofin siyasa, ta’addanci ko sauran mugayen laifuffuka.

Kara karanta wannan

Gwamna zai raba tallafin Naira biliyan 3.9, za a ba jama'a katin cire kudi

Duk da yawan sace sacen mutane da aka samu a bana, gwamnati a matakai daban daban suna ikirarin cewa suna matukar kokari kan tsaro.

Yadda gwamnoni ke yakar 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Arewa sun dauki matakan amfani da 'yan banga domin yaki da 'yan bindiga.

Rahoton Legit ya nuna cewa jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da sauransu sun dauki matakin amfani da yan sa-kai domin inganta tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng