Gwamna Zai Yafewa 'Dan Shekara 17 da Kotu Ta Yankewa Hukuncin Kisa saboda Satar Zabo
- Gwamnan Osun ya umurci bincike kan shari'ar saurayi dan shekara 17 da aka yanke wa hukuncin kisa saboda satar zabo
- Iyayen Segun Olowookere sun roki gwamnan da ya yi wa ɗansu afuwa, bayan wata kotu ta yanke masa hukunci a garin Ikirun
- Gwamnan ya tabbatar da cewa zai binciki lamarin da gaggawa domin yin adalci da kuma yiwa wanda aka yi wa saurayin afuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya shiga lamarin saurayi dan shekara 17 da aka yankewa hukuncin kisa kan satar zabo.
Gwamna Adeleke ya umurci Antoni Janar na jihar ya binciki lamarin domin tabbatar da yin afuwa ga saurayin kafin ƙarshen shekarar nan.
Gwamna ya hana rataye wani saurayi
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, gwamnan ya ce ya samu rahoto cewa an yankewa saurayin hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda satar zabo a jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Adeleke ya ce,
"Na umurci Antoni Janar da ya fara bincike da aiwatar da tsare-tsaren yin yafiya ga wannan matashin."
Ya kara da cewa jihar Osun tana kan ka’idar ta na yin adalci da kuma kare rayukan wadanda suka kamata, don haka za a bibiyi lamarin a tsanaki.
Kotu ta yankewa saurayi hukuncin kisa
Wata babbar kotun jihar Osun ce ta yankewa Segun Olowookere, wanda aka haifa a Osun hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da garkame shi a gidan yarin Kirikiri.
An yankewa saurayin hukuncin kisan ne kan zargin ya saci zabo da kwan zabuwa a wata gonar kaji da ke Odo-Otin, a cewar SaharaReporters.
Iyayen Segun Olowookere sun garzaya wajen Gwamna Adeleke da shugaban majalisar jihar domin nemawa dansu afuwa kan hukuncin da aka yanke masa.
Satar kaji: Kotu ta daure saurayi da budurwa
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa wata kotun majistare da ke da zama a Kafanchan, jihar Kaduna ta daure saurayi da budurwa kan satar kaji.
An ce matashin mai suna Abdullahi Sani tare da budurwarsa sun saci kaji 64 tare da yanke su, wanda ya saba da dokokin Penal Code na jihar Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng