CBN Ya Kayyade Kudin da 'Yan Najeriya Za Su Rika Cirewa daga Masu POS

CBN Ya Kayyade Kudin da 'Yan Najeriya Za Su Rika Cirewa daga Masu POS

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sabon tsari na rage yawan kudin da za a iya cirewa kullum daga na’urorin POS
  • CBN ya bayyana cewa wannan matakin na daga cikin shirin bunkasa tattalin arziki ta hanyar amfani da na’urorin zamani
  • Sanarwar ta shafi bankunan ajiya, kananan bankuna, da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaftace sana'ar masu na'urorin POS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya iyakance kudin da za a iya cirewa kullum daga POS zuwa N100,000 ga kowane abokin hulda.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da aka aikewa dukkan bankunan ajiya (DMBs), bankunan kananan ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Saratu Daso, El Muaz da wasu 'yan wasan Kannywood 2 da suka rasu a 2024

Contibutor
CBN ya kayyade kudin da ake cira a wajen masu POS Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa CBN ya bayyana cewa wannan na daga cikin kokarinsa na ci gaba da bunkasa tattalin arziki na bangaren rage rike takardun kudi watau ‘cashless policy.’

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN ya fitar da tsare-tsare ga bankuna

Businessday ta wallafa cewa CBN ya bayyana cewa an iyakance kudin da za a rika fitarwa domin magance matsalolin da aka gano, dakile zamba, da daidaita ayyukan masana’antar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Dukkan bankuna su tabbatar sun bin wadannan umarnin ba tare da bata lokaci ba:
"i. Masu bayar da kudi (bankuna) su tabata kudin da ake ba kowane abokin hulda bai wuce N500,000 a kowane mako ba.
“ii. Su tabbatar da cewa dukkan na’urorin POS na wakilan banki an daidaita su zuwa iyakar cire kudi na kullum na N100,000.00 ga kowane abokin ciniki.”

Bankin CBN ya iyakance kudi ga masu POS

CBN ya umurci cewa dukkan bankua su tabbatar da cewa adadin kudin da kowanne mai POS zai iya cirewa a kullum bai wuce Naira 1,200,000.00 ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta wuce gona da iri, bashin da aka karbo ya haura iyaka da N4trn

Babban bankin ya kuma tilasta cewa an aika mata da dukkan bayanan mu’amalolin kudi na yau da kullum na kowanne mai POS ya yi.

CBN ya yi gargadin hukunta duk wadanda su ka ki bin sababbin tsare-tsaren da ta fitar, wanda ya ce an yi su ne domin inganta tattalin arzikin masana’antar.

CBN ya gano masu jawo matsalar kudi

A baya, kun ji cewa babban bankin kasa (CBN) ya gudanar da bincike domin gano musabbabin karancin takardun kudi a hannun 'yan Najeriya, kuma an tabbatar da masu laifin.

CBN ya dora alhakin rashin isassun takardun kudi a kan a kan wasu bankuna da ke bai wa abokan huldarsu da masu ido da kwalli kudi fiye da sauran abokan huldarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.