Yan Sanda Sun kai Farmaki Unguwannin Kano, An Kama Manyan 'Yan Daba

Yan Sanda Sun kai Farmaki Unguwannin Kano, An Kama Manyan 'Yan Daba

  • Rundunar ‘yan sanda a Kano ta kaddamar da farmaki a unguwanni, kuma ta kama matasa 24 da ake zargi da tada hankali
  • A yayin farmakin, rundunar ta kama makamai masu hadari da dama daga hannun matasan da ake zargi cewa 'yan daba ne
  • Haka zalika jami'an tsaron sun gudanar da ayyukan wayar da kan al’umma tare da hadin gwiwar shugabannin unguwanni
  • Wani mazaunin Zango, Musa Adamu Musa ya zantawa Legit cewa suna farinciki da kama 'yan dabar domin sun addabe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kaddamar da gagarumin samame daga ranar 13 zuwa 16 ga Disamba 2024.

Rundunar ta bayyana cewa ta yi samamen ne domin dakile rikice-rikicen matasa a yankunan Kofar Mata, Yakasai, Zango, Zage, da wasu wurare.

Kara karanta wannan

Kano: An gano gidan da aka ajiye mutane domin safararsu zuwa ketare

Yan sanda
An kama 'yan daba 24 a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, ASP Abdullai Haruna Kiyawa ya wallafa yadda samamen ya gudana a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama 'yan daba 24 a jihar Kano

Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama mutane 24 da ake zargi da aikata ta’addanci, tare da kwace makamai masu hadari daga hannun su.

ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa za a gurfanar da matasan a gaban kotu bayan kammala bincike.

Dabarun yaki da daba a Kano

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana cewa sun dauki matakan tsaro na hadin gwiwa da suka hada da haduwa da masu unguwanni, dattijai, kungiyoyin sa-kai da 'yan kasuwa.

An gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a ta kafafen yada labarai irin su rediyo, talabijin, da kafafen sada zumunta.

Salman dogo
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

CP Salman Dogo Garba ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da daukar matakan tsaro domin tabbatar da doka da oda a Kano.

Kara karanta wannan

Yan sanda, sarakuna da mutanen gari sun hadu domin murkushe 'yan daba a Kano

Hanyoyin tuntubar 'yan sandan Kano

Rundunar ta ba da lambobin tuntuba ga jama’a domin kai rahoton gaggawa:

  • 08032419754
  • 08123821575
  • 09029292926

Tare da haka, rundunar ta yi kira ga al’ummar Kano su ci gaba da bayar da goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Legit ta tattauna da mazaunin Kano

Wani dan jihar Kano da ke Zango ya ce kama 'yan dabar zai kawo musu saukin rayuwar yau da kullum.

Musa Adamu Musa ya ce sau da yawa suna fuskantar barazanar rasa kayayyakinsu idan 'yan dabar suka fito fada ko kwace.

An kama 'yan fashi a jiha Kano

A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan jihar Kano ta ta samu nasara kan wasu mutane da ake zargi 'yan fashi da makami ne.

Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdulahi Haruna Kiyawa ya ce an kama mutanen ne da zargin tare hanyoyin Kano da wasu jihohi domin fashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel