Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ta Amince da Kudirin Kasafin Kudin 2025, Ta Yi Masa Gyara
- Majalisar dokokin jihar Katsina ta yi gyara ga kasafin kuɗin shekarar 2025 da Gwamna Dikko Radda ya gabatar a gabanta
- An yi wa kasafin kuɗin ƙarin Naira biliyan 10 kafin a amince da shi a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 17 ga watan Disamban 2024
- Shugaban majalisar dokokin jihar ya bayyana cewa an amince da kasafin kuɗin na Naira biliyan 692.244 ne bayan an yi nazari sosai a kansa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira biliyan 692.244.
Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban majalisar domin neman amincewa da shi.
Majalisa ta amince da kasafin kudin 2025
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an amince da ƙudurin ne a zaman majalisar na ranar Talata, wanda shugabanta, Alhaji Nasir Yahaya-Daura ya jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dikko Umaru Radda ya gabatar da kasafin kuɗi na sama da Naira biliyan 682.2 ga majalisar a ranar, 25 ga watan Nuwamba, 2024.
Sai dai a lokacin da ake kare kasafin kuɗin, kwamitin da ke kula da kasafin kuɗin ya gano rashin sanya wata Naira biliyan 10, lamarin da ya sa aka ƙara adadin kuɗaɗen da aka amince da su a ƙarshe.
Shugaban majalisar ya tabbatar da cewa kasafin kuɗin na Gwamna Radda, an yi nazari a kansa sosai kafin ƴan majalisar su amince da shi gaba ɗaya.
Majalisa za ta tantance kwamishina
Bugu da ƙari, a zaman majalisar, ta sanya lokacin tantance Alhaji Malik Anas a matsayin kwamishina da Alhaji Abdullahi Gagare a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin kuɗi ta jiha.
Majalisar ta ta gudanar da tantancewar ne a ranar Laraba 18 ga watan Disamban 2024.
Gwamna Radda ya amince da mafi ƙarancin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanat da sabon mafi ƙarancin albashin da zai riƙa biyan ma'aikatan gwammati.
Gwamna Radda ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata wanda zai fara biya daga watan Disamban 2024.
Asali: Legit.ng