Sabon Mafi Karancin Albashi: Gwamna Ya Sanya Ranar Fara Biyan Ma'aikata N80,000

Sabon Mafi Karancin Albashi: Gwamna Ya Sanya Ranar Fara Biyan Ma'aikata N80,000

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatan jihar daga Janairu, 2025
  • Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga Yulin 2024 ne amma gwamnan ya ce biyan kudin zai soma daga Janairun shekarar gaba
  • A karkashin Gwamna Seyi Makinde, ma’aikatan jihar Oyo za su ci gaba da samun albashin wata 13 wanda aka fara ba su daga 2019

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Gwamnatin jihar Oyo za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikata daga watan Janairun 2025.

Kwamishinan watsa labarai, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana cewa an cimma matsaya da ƙungiyoyin ƙwadago kan sabon albashin a ranar Talata.

Gwamnatin Oyo ta bayyana lokacin fara biyan sabon mafi karancin albashi na N80,000
Oyo: Gwamna Seyi Makinde zai fara biyan sabon albashin N80,000 daga Janairu. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

Gwamnatin Oyo za ta fara biyan N80,000

Sakataren gwamnatin Oyo, Farfesa Olanike Adeyemo da shugabar ma’aikata, Misis Olubunmi Oni, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnati, inji Tribune.

Kara karanta wannan

"Dole sai na tantance" Gwamna ya shinfida sharaɗin fara biyan albashin N80,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamared Kayode Martins na NLC da Kwamared Bosun Olabiyi na TUC, tare da wasu shugabannin ƙwadago, sun sanya hannu a madadin ma’aikata.

Yarjejeniyar ta nuna cewa sabon tsarin albashin zai fara aiki daga watan Yulin 2024 amma biyan kudin zai soma Janairun 2025.

Duk waɗanda suka yi ritaya tsakanin Yuli zuwa Disamba 2024 za a lissafta fanshonsu bisa sabon tsarin albashi.

Gwamnati na kashe N77bn wajen biyan albashi

Gwamnati ta bukaci ma’aikatu da su ƙara himma wajen tara haraji domin ƙara haɓaka samun kudaden shiga na jiha (IGR).

Kwamishinan ya bayyana cewa jihar tana kashe sama da N6bn a wata wajen biyan albashi, wanda ke zama sama da N77bn a shekara.

Ma’aikatan za su fara shekarar 2025 da sabon albashi, yayin da za su ƙare 2024 da albashin wata 13 kamar yadda aka saba tun daga 2019.

Makinde ya tsayar da sabon albashi a Oyo

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya amince zai biya ma'aikatan jihar N80,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Abba ya nada kwamishioni 6, hadimin da aka tsige zai dawo gwamnatin Kano

Amincewa da biyan N80,000 na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta amince da N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi na tarayya da jihohi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.