Shugaba Tinubu Ya Naɗa Aisha Garba a Babban Muƙamin Gwamnatin Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Aisha Garba a Babban Muƙamin Gwamnatin Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Aisha Garba a matsayin shugabar hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta kasa watau UBEC
  • Aisha Garba, mace ce da ta yi fice a fannin bunkasa harkokin ilimi na ƙasa da ƙasa, ta shafe shekaru tana aiki da bankin duniya
  • Tinubu ya bayyana cewa yana fatan sabuwar shugabar UBEC za ta jagoranci hukumar wajen bunkasa harkokin ilimin yara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Aisha Garba a matsayin shugabar hukumar kula da ilimin bai ɗaya (UBEC) ta kasa.

Bola Tinubu ya naɗa Aisha, ƙwararriya a fannin kawo ci gaba ta ƙasa da ƙasa, a wani ɓangare na kokarin farfaɗo da bangaren ilimi a Najeriya.

Shugaba Tinubu.
Bola Tinubu ya naɗa mace a matsayin shugabar UBEC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Ku ƙara imani da Allah SWT," Gwamna ya yi magana bayan gobara ta laƙume miliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin midiya ne ya wallafa sanarwar a shafin X.

Taƙaitaccen bayani kan Aisha Garba

Aisha Garba da ke aiki da bankin duniya ta shafe shekaru 24 tana ba da gudummuwa a fannin ilimi a Najeriya, Ghana, Amurka, Somalia, Kenya da Burtaniya.

A shekaru 15 da ta yi tana aiki da bankin duniya, Aisha ta nuna gogewa da ƙwarewa wajen tsare-tsaren bunƙasa ilimi tun daga matakin farko har aiwatarwa.

Ta yi karatun digirin farko a fannin Turanci da na'ura mai kwakwalwa a jami'ar Petra American da ke ƙasar Jodan.

Aisha Garba ta kuma karɓi takardar shaidar kammala digiri na biyu a Jami'ar Birmingham da ke ƙasar Burtaniya.

Shugaba Tinubu ya yi mata fatan nasara

Shugaba Tinubu ya ce yana fatan Aisha za ta jagoranci UBEC wajen aiwatar da manufar gwsmnatinsa na samar da ilimi mai inganci da ƙananan yaran Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya naɗa mutane 8 a muhimman muƙamai

Tinubu ya na kuma fatan za ta bunƙasa ilimi ta yadda ƴan Najeriya za su shiga a fafata da su a matakin duniya.

Tinubu ya naɗa manyan sakatarori 8

Rahoto ya gabata cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ƙarin manyan sakatarori takwas da za su cike gurbin da ake da su a hukumar kula da ma'aikatan tarayya.

Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu ya bukaci sakatarorin su yi aiki tukuri wajen sauke nauyin amanar da aka ɗora masu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262