Mutane Sun Shiga Dimuwa da Yan Bindiga Suka Bindige Babban Lakcara a Jami'a
- Wani malamin Jami'a ya gamu da ajalinsa yayin da wasu da ake zargin masu kwace mota ne suka bindige shi
- Lamarin ya faru ne a daren jiya Litinin 16 ga watan Disambar 2024 da marigayin, Dr. Fabian Osita ke komawa gida
- Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin yana koyarwa a Jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke birnin Awka a Anambra
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Anambra - Wasu da ake zargin masu kwacen motoci ne, sun harbe wani malamin Jami’a a jihar Anambra.
Maharan sun bindige malamin ne da ke Jami'ar Nnamdi Azikiwe, Awka mai suna Dr Fabian Osita.

Asali: Original
Yan bindiga sun bindige lakcara a Anambra
Punch ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Litinin 16 ga watan Disambar 2024 a cikin birnin Awka.

Kara karanta wannan
Tsohon gwamna a Adamawa ya ba da cin hanci domin zarcewa a karo na 2? Gaskiya ta fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya faru ne lokacin da marigayin ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya tashi daga wurin aiki.
Wani shaidar gani da ido ya ce maharan sun tare lakcaran domin su kwace motarsa, amma ya yi ƙoƙarin jayayya sai kawai suka harbe shi a kai.
“Eh, sun harbe shi a wurin 'High Tension' a yammacin jiya Litinin, wasu na cewa shi malami ne a Jami’ar UNIZIK, kuma ɗan asalin Nteje ne."
“Maharan sun tare motarsa kirar Toyota Corolla yayin da yake tuka motar, suka yi yunƙurin kwacewa, amma ya yi yunƙurin turjiya, hakan yasa suka harbe shi a kai, kuma nan take ya rasu."
“Barayin sun bar gawarsa suka tafi da motarsa, ya rasu kafin wani ya zo domin taimakonsa."
- Cewar majiyar
Matakin da ƙungiyar ASUU ta ɗauka
Shugaban tsaro na Jami’ar, Ken Chukwurah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an harbe shi ne da misalin karfe 7:30 na yammacin Litinin.
Chukwurah ya ce kungiyar ASUU reshen jami’ar suna shirye-shiryen zuwa Gidan Gwamnati a Awka domin nuna rashin jin dadinsu kan tabarbarewar tsaro.
Al'umma sun nemi addu'o'i da Fasto ya bata
A baya, kun ji cewa al'ummar jihar Anambra sun shiga jimami bayan bacewar wani babban malamin addinin Kirista.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Rabaran Godwin Okpala ya bace yayin da yake kan hanyar zuwa garin Umuchu a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng