'Ka Kawo Cigaba a Najeriya': Jonathan Ya Tura Sakon Yabo da Buhari Ya Cika 82
- A yau Talata 17 ga watan Disambar 2024, tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekaru 82 a duniya
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya taya Buhari murnar wannan rana ta zagayowar ranar haihuwarsa
- Jonathan ya yi masa fatan samun karin lafiya da kwanciyar hankali inda ya yaba masa kan cigaban da ya kawo kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya taya Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Goodluck Jonathan ya taya Muhammadu Buhari murna ne bayan ya cika shekaru 82 tare da yi masa fatan alheri da lafiya da kwanciyar hankali.

Asali: Facebook
Jonathan ya yaba salon mulkin Buhari
Jonathan ya bayyana hakan a cikin wata sakon taya murna da ya sanyawa hannu a yau Talata 17 ga watan Disambar 2024, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Ana shirin ballowa tsohon gwamna ruwa, ya yi barazana ga masu son hada shi da Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya yabawa Muhammadu Buhari kan rawar da ya taka wajen tabbatar da hadin kai da cigaban kasa.
“A madadin ni kai na da iyalaina, ina mika sakon taya murna gare ka a wannan rana ta musamman.'"
"A wannan rana ta haihuwa, ina addu’a Allah ya ba ka lafiya, hikima da farin ciki.
“Ina kuma amfani da wannan dama don jaddada yabo ga jajircewarka wajen cigaban kasa da bunkasarta."
- Goodluck Jonathan
Jonathan ya yi wa Buhari fatan alheri
Yayin da yake masa fatan farin ciki a wannan rana ta musamman, Jonathan ya yi masa fatan kusanci da masoyansa, The Nation ta ruwaito.
“Ina fatan wannan sabuwar shekara a rayuwarka za ta kara kusanci tsakaninka da masoyanka."
"Ina kuma fatan ranar haihuwarka ta kasance cike da kauna da farin ciki, ka karbi sakon taya murna ta musamman a wannan ranar haihuwarka.”
- Goodluck Jonathan
Basarake ya yabawa mulkin Buhari
Kun ji cewa fitaccen basarake a Kudancin Najeriya ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Katsina.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yabawa tsohon shugaban kasar lokacin da yake mulkin Najeriya da cewa ya taka rawa .
Basaraken ya ce abin mamaki Buhari ya kara murmurewa kaman wani matashi duk da shekarun da yake da shi a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng