Shugaban Majalisa Ya Zauna da Jagorori, Ana Son Amicewarsu don Kudirin Haraji Ya Tabbata
- Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya na neman tattaro kan 'yan majalisa a kan kudirin harajin Tinubu
- Kudirori hudu ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika wa majalisun kasar nan, lamarin da ya yamutsa hazo matuka
- Amma an samu rahoton kakakin majalisa, ya zauna da shugabanni daga shiyyoyin kasar nan shida don su amincewa da kudirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas, ya gana da shugabannin shiyyoyin kasar nan shida da sakatarorinsu a majalisa domin neman su amince da kudirin harajin Tinubu.
Kudirorin yi wa dokar harajin kasar nan gyara guda hudu da shugaban Bola Ahmed Tinubu ya aika majalisun kasar nan sun jawo ce-ce-ku-ce da tirjiya daga sassan Najeriya.

Source: Facebook
Rahoton da ya kebanta da Daily Nigerian ya bayyana cewa Tajuddeen Abbas ya samu ganawa da wakilai shida a ranar Litinin domin cusa masu amincewa da kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haraji: Shugaban majalisa ya zauna da shugabanni
An samu rahoton cewa Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya na son shugabannin shiyyoyin kasar nan na majalisa da su amince domin kudirin harajin Tinubu kar ya samu matsala.
Daga wadanda su ka halarci taron akwai Sada Soli daga Arewa maso Yamma; Mukhtar Betara daga Arewa maso Gabas; Ahmed Wase daga Arewa ta Tsakiya.
Sai kuma Fredrick Agbedi daga Kudu maso Kudu; James Faleke daga Kudu maso Yamma; da Igariwey Iduma daga Kudu maso Gabas.
Ana son tabbatar da kudirin haraji a majalisa
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas na son ‘yan majalisa su bayar da hadin kai don tabbatar da kudirin harajin Tinubu.
An gano Rt. Hon Abbas na son kudirin ya tsallake karatu na biyu a zaman da majalisa za ta yi a yau.

Kara karanta wannan
Arewa da Kudu: Yadda kudurin harajin Tinubu ya raba kan 'yan majalisa da manyan Najeriya
Gwamnati ta fadi dalilin mika kudirin haraji
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ta bayyana dalilan da suka sa ta bijiro da kudirin gyaran dokar haraji har guda hudu a kasar nan.
A jawabin hadimin Bola Tinubu a kan sadarwa, Sunday Dare ya ce dokar za ta warware matsalolin tattalin arziki da saukaka haraji ga talaka da kananan 'yan kasuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
