Gwamna ya Dura kan Tinubu, Ya ce ba Zai yi Aiki da Tsare Tsaren 'T Pain' ba
- Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya ce manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun jefa 'yan Najeriya a masifa
- Mai girma Oborevwori ya ce an gaza samun wata fa'ida kan cire tallafin man fetur da karya darajar Naira da Bola Tinubu ya yi a bara
- Sheriff Oborevwori ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta fitar da manufofin da za su rage talauci da wahalhalun rayuwa a kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana damuwarsa kan tsare tsaren tattalin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan Delta ya ce yunwa, talauci, da rashin aikin yi sun karu sakamakon tsare tsaren Tinubu na cire tallafin man fetur da karya darajar Naira.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Felix Ofou ya fitar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya kawo yunwa inji Gwamanan Delta
Gwamna Oborevwori ya bayyana cewa duk wani amfani da aka yi tsammanin samun bayan cire tallafin man fetur an rasa shi saboda matsalar karyewar Naira da hauhawar farashi.
“Menene amfanin karin kudi da ake yi wa jihohi idan aka kwatanta da hauhawar farashi, faduwar darajar naira, yunwa mai tsanani, talauci, da rufe manyan masana’antu a kullum?”
- Gwamna Sheriff Oborevwori
Gwamnan ya yi maganar ne bayan kalaman tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya ce tsare tsaren Tinubu sun kawo karin kudin shiga ga jihohi.
Daily Post ta rahoto cewa Oborevwori ya ce Bankin Duniya da IMF sun ce tsare tsaren Tinubu ba su aiki, kuma sun mayar da Najeriya babban birnin talauci a duniya.
Ya kara da cewa tsarin Tinubu ba hanya ce da jama’ar Delta za su amince da ita ba, kuma ba za su yi koyi da salon APC na wahalar T-pain ba.
An bukaci yin taron dangi ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon jagora a APC, Salihu Lukman ya bukaci a yi gagarumar hadaka domin kayar da Bola Tinubu a zaben 2027.
Salihu Lukman ya bukaci Obasanjo ya hada kan tsofaffin shugabanni da suka hada da Janar Ubrahim Babangida da Goodluck Jonathan wajen hadakar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng