Manyan Sarakunan Arewa da Suka Fuskanci Kalubale daga Gwamnoni a 2024
Wasu daga cikin manyan sarakunan Arewa sun yi ta fama da gwamnonin johohi a kan shugabanci a shekarar 2024
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shekarar 2024 ta kasance cike da ce-ce-ku-ce kan shugabancin gargajiya a wasu manyan jihohin Arewa musamman Kano da Sokoto.
A Kano, rikici ya biyo bayan sauke wasu sarakuna da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya nada, yayin da Sokoto ta shiga rudani kan rade-radin tsige Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku bayanai kan wadannan lamuran da yadda suka gudana a jihohi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dambarwar sarautar gargajiya a jihar Kano
Rikicin sarautar gargajiya a jihar Kano ya dauki hankali musamman yadda aka samu sarakuna biyu kowa na ikirarin rike da sarauta.
Lamarin ya faru ne bayan Abba Kabir Yusuf ya dawo da mai martaba Muhammadu Sanusi II shi kuma mai martaba Aminu Ado Bayero na ikirarin zama sahihin sarki.
Zancen sauke sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gamu da sauke shi daga mukaminsa bayan wata doka da majalisar dokokin Kano ta tabbatar.

Asali: Facebook
Wannan dokar ta rusa masarautun da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira, tare da mayar da tsarin gargajiya na masarauta daya a Kano.
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa, dokar ta bai wa gwamna damar nada sabon sarki bayan tantancewa.
Dawowar mai martaba Sanusi II
Muhammadu Sanusi II, wanda Ganduje ya sauke a 2019, ya dawo fadar masarautar Kano bayan an tsige Aminu Ado Bayero.
A lokacin da aka dawo da shi, gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarci taron da ya tabbatar da dawowarsa.

Kara karanta wannan
Lokuta 3 da Gwamnatin Tarayya ta fifita Aminu Ado kan Sanusi II a rikicin sarautar Kano
Sanusi II ya kasance daya daga cikin manyan sarakunan Najeriya da aka sani da bayyana ra’ayoyi kan harkokin siyasa da tattalin arziki.
Komawar Aminu Ado Kano bayan tsigewa
Aminu Ado Bayero ya sake komawa Kano bayan an tsige shi, inda aka ce ya yi kokarin dawowa fadar masarautar.
Wannan matakin ya jawo martani daga gwamnatin Kano, wadda ta bayyana shi a matsayin yunkurin tayar da rikici.
Abba ya umarci a kama Aminu Ado Bayero
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a kama Aminu Ado Bayero bisa zargin kokarin komawa fadar masarautar ba tare da izini ba.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da umarnin da gwamnan ya yi.
Kotu ta hana kama Aminu Ado Bayero
Biyo bayan umarnin Abba Kabir, kotun tarayya ta yi hukunci da hana kama mai martaba Aminu Ado Bayero.
Punch ta wallafa cewa bayan hukuncin hana kama Aminu Ado, kotun ta umurci gwamnatin Kano ta biya Naira miliyan 10 a matsayin diyya ga basaraken.

Kara karanta wannan
Kotu ta dakile Ganduje, ta ba da umarni ga jami'an tsaro kan cafke kakakin Abba Kabir
Aminu Ado da gwamnatin Kano a kotu
Yanzu haka, gwamnatin Kano da Aminu Ado Bayero suna gaban kotu kan rikicin tsigesa da ka yi yaki yarda.
Mutane da dama suna kallon rikicin ta bangaren siyasa inda ake ganin Aminu Ado na samun goyon baya daga gwamnatin tarayya.
Sokoto: Rade radin tsige sarkin Musulmi
Bayan jihar Kano, Sokoto ta shiga rudani kan sarauta musamman a kan rade radin tsige mai alfarma sarkin Musulmi.

Asali: Facebook
Rikicin sarauta a jihar Sokoto ya dauki hankali ne lura da cewa Sarkin Musulmi na jagorantar harkokin Musulunci a dukkan jihohi.
Maganar Shettima kan rade radin tsige Sultan
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya gargadi gwamnatin Sokoto kan rade-radin yunkurin tsige Sultan Sa'ad Abubakar III.
Sanata Kashim Shettima ya ce Sultan ba kawai shugaban gargajiya ba ne, har ma da wani ginshiki na dunkulewar Musulmai a Najeriya.
MURIC ta yi kargadi kan tsige Sultan
Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC, ta soki kudirin gyaran doka a jihar Sokoto da ta ce zai rage ikon Sultan

Asali: Twitter
Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya ce dokar za ta kawo cikas ga martabar sarautar Sarkin Musulmin a Najeriya.
Tsige Sultan: Martanin gwamnatin Sokoto
Vanguard ta wallafa cewa gwamnatin Sokoto ta musanta zargin yunkurin tsige Sultan, tana mai cewa rade-radin ba gaskiya ba ne.
Ta kuma bukaci Mataimakin Shugaban Kasa da ya duba gaskiyar al’amura kafin yin jawabi a kan batutuwan da suka shafi jihar.
Sauyin shugabancin gargajiya a Adamawa
A jihar Adamawa ma an samu rudani yayin da aka zargi gwamnati da shirya rage karfin iko ga Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha.
Kirkirar sababbin masarautu Adamawa
Majalisar dokokin Adamawa ta zartar da doka da ta samar da sababbin masarautu tare da karin hakimai.
Rahotanni sun nuna cewa sabuwar dokar za ta bai wa gwamna damar nada ko tsige sarakuna a jihar.

Asali: Facebook
Sabuwar dokar ta bar Lamidon Adamawa a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar, amma ta mayar da tsarin shugabancin karba-karba a yankunan jihar kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Zargin tsige Lamido Adamawa
Majalisar dokokin Adamawa ta musanta rade-radin cewa sabuwar dokar na da nufin tsige Lamido Adamawa.
Majalisar ta bayyana cewa tsarin karba-karba na da nufin samar da daidaito a tsakanin sarakunan jihar.
Maganar 'Dan Sanusi kan rigimar sarauta
A wani rahoton, kun ji cewa Adam Lamido Sanusi ya nuna damuwa kan yadda mahaifinsa ke fuskantar kalubale a sarautar Kano.
Adam Lamido ya yi magana ne bayan 'yan sanda sun mamaye fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II a makon da ya wuce yana shirin fita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng