An Samu Matsala, Tinubu Ya Dakatar da Gabatar da Kasafin Kudin 2025

An Samu Matsala, Tinubu Ya Dakatar da Gabatar da Kasafin Kudin 2025

  • Rahotanni da suka fito na nuni da cewa shugaba Bola Tinubu ya dakatar da gabatar da kasafin da aka sa zai yi a gobe a Talata
  • Bayanai da suka fito daga majalisa sun tabbar da cewa shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin a ranar Laraba mai zuwa
  • Dama dai an tsara za a gudanar da taron ne a zauren Majalisar Wakilai tare da haɗin gwiwar Majalisar Dattawan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - An dage ranar gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2025 daga ranar Talata, 17 ga Disamba, zuwa ranar Laraba, 18 ga Disamba, 2024.

Tun a karon farko, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar a da cewa shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta wuce gona da iri, bashin da aka karbo ya haura iyaka da N4trn

Tinubu
Tinubu ya dage gabatar da kasafin kudi. Hoto: Aso Villa
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa matakin ya biyo bayan sanarwar da aka samu ne daga wani babban jami’in Majalisar Tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani kan dage gabatar da kasafi

Leadership ta wallafa cewa wani jami’i daga cikin ma’aikatan majalisar ya bayyana cewa za a fitar da sanarwa a hukumance game da dagewar nan da ‘yan sa’o’i masu zuwa.

Tun da farko, Godswill Akpabio ya ce an riga an tsara yadda shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗi na N47.9tn a wani zaman haɗin gwiwar majalisun tarayya biyu.

Ana hasashen an dage gabatar da kasafin ne saboda yin gyaran da zai ba da damar samun tsari mafi inganci.

Tsarin gabatar da kasafin kuɗin 2025

Bola Tinubu zai gabatar da kasafin ne a zauren Majalisar Wakilai da karfe 10:30 na safe kamar yadda tsare tsaren farko suka nuna

Sanata Akpabio ya ce Sanatoci za su fara taruwa ne a Majalisar Dattawa kafin su tattara zuwa Majalisar Wakilai cikin tsari na musammam domin karɓar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga matsala da ake zargin an handame N57bn a ma'aikata, ana tuhumarsa

Kasafin kuɗin 2025 na da muhimmanci domin sanin yadda gwamnatin shugaba Tinubu za ta tafiyar da kuɗin Najeriya a shekara mai zuwa.

Gwamnan Neja ya gabatar da kasafin N1.5tn

A wani rahoton, kun ji cewa Mai girma gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga majalisa.

Gwamna Umaru Bago ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 1.5 kuma ya bayyana muhimman ayyukan da kasafin zai mayar da hankali a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng