Babban Hafsan Tsaro Ya ba da Umarnin Bincike kan Mutuwar Shugabanni 2 a Hannun Sojoji

Babban Hafsan Tsaro Ya ba da Umarnin Bincike kan Mutuwar Shugabanni 2 a Hannun Sojoji

  • Babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa ya ba da umarnin bincike kan mutuwar shugabannin Okuama
  • A ƴan makonnin da suka wuce ne jagororin Okuama a jihar Delta suka sanar da mutuwar shugabanninsu biyu a hannun sojoji
  • Wannan ya sa CDS ya sa a yi bincike don gano gaskiyar lamarin kafin ɗaukar matakin da ya dace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar shugabannin Okuama biyu a hannun sojoji.

Shugaban al'ummar garin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli a jihar Delta, Pa James Oghoroko da ma'aji Dennis Okugbaye, sun mutu ne a hannun dakarun soji.

CDS Christopher Musa.
Babban hafsan hafsoshin ƙasar nan ya ba da umarnin bincike kan mutuwar shugabannin Okuama a hannun sojoji Hoto: @DefenceinfoNG
Asali: Facebook

Babban Hafsan tsaro ya sa a yi bincike

Kamar yadda Punch ta ruwaito mutanen biyu sun rasa rayukansu ne watanni uku bayan kama su tare da wasu jagororin al'ummar Okuama.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun shiga alhini, sun yi ta'aziyyar mutuwar mutane a hadarin jirgin Binuwai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamen dai ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa sojoji 17 ranar 14 ga watan Maris, 2024 sa'ilin da suka je aikin sasanta rikicin Okuama da ƙauyen Okoloba.

Da yake magana kan lamarin a karon farko, babban hafsan hafsoshin kasar nan (CDS) ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan mutuwar shugabannin Okuama.

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar soji ta ƙasa, Birgediya Tukur Gusau ne ya bayyana hakan a wurin taron kwamitin sadarwa na ƙarshen shekara a Abuja.

Wane mataki hukumar sojoji za ta ɗauka?

Ya ce CDS Musa ya umarci rundunar sojin ƙasa ta 6 ta gudanar da bincike kan lamarin, kuma ta miƙa masa rahoto ranar Litinin, rahoton Vanguard.

"Dangane da batun mutuwar mutane a tsare a hannun sojoji, mun samu labarin cewa wasu shugabannin al'umma da aka tsare game kan abin da ya faru a Okuama sun mutu."
"Nan take CDS ya umarci rundunar soji ta 6 ta gudanar da bincike kan lamarin, saboda haka kowane lokaci daga yanzu muna sa ran rahoton bincike don tabbatar da gaskiya ko akasin haka."

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya jero manyan kasa da suka halarci auren 'ya 'yansa, ya yi musu godiya

"A halin yanzu dai batun cewa shugabannin sun mutu a hannun sojoji duk zargi ne kawai, amma za mu gano gaskiya, zuwa gobe za ku ji ƙarin bayani."

- Tukur Gusau.

DHQ ta musanta batun kawo sojojin Faransa Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hedkwatar tsaron Najeriya watau DHQ ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa za a kafa sansanin sojojin Najeriya a ƙasar nan.

DHQ ta bayyana cewa labarin ƙarya ce da wasu masu son tada fitina suka kirkira, sannan ta buƙaci ƴan Najeriya su yi fatali da jita-jitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262