Matatar Dangote Ta Fara Fitar da Fetur zuwa Kasashen Afrika 4
- Matatar Dangote ta fara fitar da man fetur zuwa kasashe hudu a nahiyar Afrika, wanda ya hada da Kamaru, Angola da Ghana da Afrika ta Kudu
- Bayanin ya fito ne daga mataimakin shugaban sashen man fetur da gas na Dangote, Devakumar Edwin a zantawarsa da jakadan Japan
- Devakumar Edwin ya kara da bayar da tabbacin cewa matatar Dangote za ta ci gaba da tabbatar da bin ka'idojin duniya wajen samar da mai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Matatar Dangote ta fara fitar da man fetur zuwa kasashen Kamaru, Angola, Ghana, da Afirka ta Kudu a makonnin da suka gabata.
Mataimakin shugaban sashen man fetur da gas na Dangote, Devakumar Edwin, ya bayyana haka yayin karbar bakuncin wata tawaga daga al’ummar kasuwanci ta kasar Japan a Najeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe a sanarwar da kakakin kamfanin Anthony Chiejina, inda ya ce Edwin ya tabbatar wa jakadan Japan, Suzuki Hideo feturin matatar ya cika ka’idojin duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana fitar da man jirgin Dangote zuwa Turai
The Street journal ta wallafa cewa matatar Dangote ta fara fitar da man jiragen sama zuwa kasashen Turai, kamar yadda Devakumar Edwin ya bayyana.
Mataimakin shugaban sashen man fetur da gas na Dangote ya ce;
“A cikin makonni kadan da suka wuce, mun fitar da man fetur zuwa Kamaru, Ghana, Angola, da Afirka ta Kudu, da sauransu.
"Diesel kuma ya kai ga kasashen duniya, sannan man jirgin sama ana fitar da shi sosai zuwa kasuwannin Turai. Kayayyakinmu sun fara yin suna a duniya.”
“Matatar Dangote na kara bunkasa,” Edwin
Devakumar Edwin ya tabbatar wa jakadan Japan da tawagarsa cewa kamfanin a shirye yake don yin hadin gwiwa tare da kokarin ci gaba da kiyaye mafi kyawun ka’idoji.
Ya ce zai kara jawo jarin da za a zuba a bangaren masana’antu na sarrafa albarkatun kasa, wanda zai kara daga darajar bangaren.
Dangote ya fara fitar da fetur zuwa ketare
A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar Dangote ta fara fitar da man fetur zuwa makwabciyar Najeriya, inda ta kara kulla yarjejeniya da kamfanin Neptune Oil na kasar Kamaru.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote bayyana jin dadinsa da irin hadin gwiwar da wanda ake sa ran zai habaka tattalin arzikin kasashen Najeriya da kamaru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng